Rasuwa
Fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Dokta Yusuf Ali ya rasu
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/11/Screenshot_20231106-102335_1.jpg)
Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Dokta Yusuf Ali rasuwa.
Sheikh Dokta Yusuf wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya ya rasu ne a daren lahadi bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73.
‘Yar marigayin, Dokta Bilkisu Yusuf Ali ta shaidawa Aminiya cewa za a yi janaizarsa a yau Litinin da Azabar a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo.
Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alkali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban a Jihar Kano, kafin ya yi ritaya a shekarar 2009.
Bayan koyarwar addinin da ya ɗauki tsawon lokaci yana yi, malamin ya yi tashe wajen taimaka wa al’umma ta ɓangaren neman lafiya daga shafar aljanu.
Ƙasashen Waje
Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu
![Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG-20240702-WA0041.jpg)
Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu
Daga Ibraheem El-Tafseer
Frane Selak ya kasance wanda ya fi kowa tsallake rijiya da baya a duniya.
A shekarar 1962 ya tsallake haɗarin jirgin ƙasa wanda mutane 17 suka mutu, a 1963 jirgi ya faɗi da shi kowa ya mutu sai shi kaɗai ko ƙwarzane bai yi ba.
A shekarar 1966 motar safa ta lume da su a rafi mutum huɗu sun mutu amma Frane bai samu ko ƙwarzane ba a yayin da a shekarar 1973 motarsa ta kama da wuta ya tsallake rijiya da baya, ya kuma tsallake haɗarin taho mu gama da mota ta yi da shi ya tsira ya kuma lashe yuro dubu ɗari takwas a Caca a shekarar 2003.
KU KUMA KARANTA: Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki
Rasuwa
Allah Ya yi wa matar mataimakin gwamnan Neja rasuwa
![Allah Ya yi wa matar mataimakin gwamnan Neja rasuwa](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG_6198-637x430-1.jpeg)
Allah Ya yi wa matar mataimakin gwamnan Neja rasuwa
Hajiya Zainab ta rasu ne a asibiti bayan gajeruwar rashin lafiya.
Mutuwa ta riske ta ne a wani asibiti da ke Minna, babban birnin jihar a ranar Talata.
Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana alhini da game da wannan rashi.
Sakon ta’aziyyar da kakakinsa, Bologi Ibrahim, ya sa wa hannu ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar.
KU KUMA KARANTA: Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff rasuwa
Ya kuma yi addu’a Allah Ya sada ta da mafificin rahama a Aljanna Firdausi, Ya ba wa mijinta hakurin jure wannan rashi.
Rasuwa
Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff rasuwa
![Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff rasuwa](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/Ali-Modu-Sheriffs-Mother-Dies-At-93-920x555-1.jpg)
Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff rasuwa
Mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ta riga mu Gidan Gaskiya.
Mahaifiyar tsohon gwamnan, Hajja Aisa, ta koma ta Mahaliccinta ne a ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin jihar.
Ta rasu tana da shekaru 93, bayan fana da rashin lafiya.
Sanarwar rasuwar ta bayyana cewa za yi jana’izar Hajja Aisa da Azahar ranar Litinin 1 ga watan Yuli, 2024.
KU KUMA KARANTA: Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa
Za a yi jana’izar ne a gidant Marigayi Galadima Modu Sheriff d da ke Damboa Road a Maiduguri.
Sanarwar ta kuma roka wa marigayiyar gafara da kuma Aljannatul Firdaus.
-
Kotu1 year ago
Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida
-
Labarai9 months ago
Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum
-
Ƙasashen Waje1 year ago
Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar
-
Labarai1 year ago
‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano