FIRS ta tara harajin naira tiriliyan 5.5 cikin wata shida

0
189

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Najeriya (FIRS) ta bayyana karɓar harajin naira tiriliyan 5.5 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Shugaban hukumar Muhammad Nami ne ya bayyana haka a lokacin taron Majalisar tattalin arziƙin ta ƙasar da ya gudana ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar de ke Abuja.

Wannan ne karo na farko da hukumar ta tara adadi mafi yawa na kuɗin haraji a cikin wata shida, kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar.

Rahoton da Muhammad Nami ya gabatar wa majalisar tattalin arziƙin, ya nuna cewa abin da hukumar ta tara ya zarta abin da ta ƙiyasta samu a cikin rabin shekarar.

KU KUMA KARANTA: Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA

Tun da farko hukumar ta ƙiyasta tara naira tiriliyan 5.3 a cikin wata shidan farko na shekarar.

Rahoton ya kuma nuna cewa kuɗin harajin da hukumar ta tara a ɓangaren man fetur, naira tiriliyan 2.03 ne ya fi yawa cikin harajin da hukumar ta tara.

Sai kuma naira tiriliyan 3.76 da hukumar ta tara daga sauran ɓangarori.

Leave a Reply