Fasinja ya yanki jiki ya faɗi ya mutu a cikin mota a Ogun

0
30
Fasinja ya yanki jiki ya faɗi ya mutu a cikin mota a Ogun

Fasinja ya yanki jiki ya faɗi ya mutu a cikin mota a Ogun

Wani fasinja ɗan shekara 29 mai suna Anuoluwapo Aderemi ya faɗi ya mutu a cikin wata motar bas ta haya a jihar Ogun.

Daily Trust ta rawaito cewa Aderemi na tafiya ne a cikin wata motar bas ta haya daga filin ajiye motoci na Papalanto da ke ƙaramar hukumar Ewekoro a jihar Ogun zuwa Ibadan, jihar Oyo.

Lamarin ya faru ne a wani gidan mai da ke Itori da misalin ƙarfe 7:45 na yammacin ranar Talata.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Odutola Omolola, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce direban bas, Akeem Olorode ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda.

“Direban na kan hanyar zuwa Ibadan ne a wata motar bas mai daukar fasinjoji 18, amma fasinjoji15 ne kawai su ka taso daga Papalanto.

“Da misalin karfe 7:00 na dare direban ya tsaya a wani gidan mai da ke Itori domin ya kara mai. Yayin da ake cika tankin, wasu fasinjojin suka sanar da shi cewa daya daga cikin fasinjojin ya yi wani abin ban mamaki kuma ya sume.

KU KUMA KARANTA:Mutum ɗaya ya mutu, biyu sun jikkata a wani haɗarin mota a Ogun

Odutola ya ce yayin da sauran fasinjojin su ka yi yunkurin ba da agajin gaggawa, tuni Aderemi ya fadi ya mutu a cikin motar.

Ya ce da samun rahoton an aika jami’an ‘yan sanda daga sashin Ewekoro zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka gano marigayin tare da wasu fasinjoji.

“Daga baya an bayyana cewa marigayin mazaunin Ibadan ne. An kai shi asibitin jihar da ke Ifo, inda wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here