Fasahar AI ba barazana ba ce ga aikin jarida, Injiniya Abbas Abdullahi

0
58
Fasahar AI ba barazana ba ce ga aikin jarida, Injiniya Abbas Abdullahi

Fasahar AI ba barazana ba ce ga aikin jarida, Injiniya Abbas Abdullahi

Daga Idris Umar, Zariya

A wajan wannan taro shi Injiniya Abbas Abdullahi ya bayyana cewa fasahar AI ba barazana ba ce ga ci gaban al’umma. Inda ya jaddada cewa fasahar AI za ta inganta ne da sauƙaƙawa al’umma wajen gudanar da ayyukan su ciki kuwa harda ƴan jarida.

Injiniya Abbas ya bayyana hakan ne a yayin taron da jaridar Almizan ta shirya na murnar cika shekaru 35 da kafa ta.

Bikin na bana na gudana ne a garin Kano wanda aka soma a daren ranar Juma’a 10 ga watan Janairun 2025 bayan isowar baƙi daga garuruwa daban-daban.

A taron na yau Asabar 11 ga watan Janairun 2025 wacce ta kasance a rana ta biyu da soma wannan taro, Injiniya Abbas Abdullahi ya gabatar da jawabi a kan maudu’i mai taken: Fasahar AI: amfani da matsalolinta.

KU KUMA KARANTA:‘Yan kwana-kwana na ci gaba da yaƙi da gobarar daji mafi girma a Amurka

Injiniya ya yi tilawar tarihi da asalin fasahar AI, inda ya yi kawo bayanai dangane da yadda za a ribaci fasahar ta AI da kuma illolinta. Sai dai ya jaddada cewa fasahar AI ci gaba ne kamar ci gaban sauran fasahohi da aka samu.

Ya jaddada cewa ƴan jarida za su iya ribatar fasahar AI ta hanyoyi da dama wanda ya haɗa da rubutu, gyarawa, tantance bayanai da labarai, tantance hotuna da bidiyo, gyaran rubutu, bidiyo, da murya da sauran ayyukan da suka shafi ƴan jarida.

Bayan ya kammala jawabinsa, mahalarta sun gudanar da tambayoyi, ƙarin bayani da nazari, daga ƙarshe aka tafi sallah da cin abinci.

Ana ci gaba da taron har zuwa ranar Lahadi.

Leave a Reply