Farashin kayan masarufi a Kasuwar Ɗambatta da ke jihar Kano
Daga Shafa’atu Dauda
A wannan makon mun shiga kasuwar ta Ɗambatta duba da gabatowar watan Azumin Ramadan, kayan abinci sun yi sauƙi saɓanin makon da ya gabata.
A yayin tattaunawar da wakiliyar Neptune prime Hausa tayi ta Sectaryn Kungiyar Ma’auna ta Karamar Hukumar Dambatta Ibrahim Aminu Ilu ya Tabbatar mana Da Insha Allah Za’a Sami sassauci Sosai na Kayan Masarufi a Cikin Kasuwar su
Inda Yace mana A satin daya gabata an Saida
Buhun Farin wake a 110,000
Amma a Wannan Satin ana sai dashi 105,000,104,000
Kwano 2600
A satin daya Wuce an Saida Buhun Masara a 60,000
Amma a wannan satin Ana Saida ita a 57,000
Kwano 1500
A satin daya Wuce an Saida Buhun waken Suya 100,000
A wannan satin Kuma ana saidashi a
95,000
Kwano 2500
KU KUMA KARANTA:Farashin kayan masarufi a kasuwar Ɗambatta dake jihar Kano
Alkama A satin daya Wuce an Saida Buhun ta 102,000
Amma a wannan satin Ana Saida ta 95,000
Kwanonta 2500
Rogo a satin daya Wuce ana saidashi 50,000 55,000
Amma a wannan satin Ana Sai dashi 45,000
Kwano 900
Gero a satin daya gabata an saidashi 62,000
Amma a wannan satin Ana Saida 57,000
Kwano 1500
Dawa A satin daya gabata an saidata 56,000
Inda a wannan satin ake Saida ita 52,000
Kwano 1400
Bayan Gama Tattaunawar mu da Ibrahim Aminu Ilu Mun Zanta da Wani Dattijo Mal.Amadu Halliru Wanda yazo Siyayya A wannan kasuwa Kuma ya nuna Farin Cikinsa na Samun Saukin Kayan Masarufin yakara da Cewa “Da Kamar Yadda aka samu Saukin kayayyaki a Wannan kasuwa ta Dambatta Sauran kasuwannima Za a samu wannan Saukin to tabbas da talaka Zai Sami Saukin wannan Kuncin Rayuwar da yake Ciki”
Allah yakara Saukaka mana Amen