Farashin kayan masarufi a kasuwar Ɗambatta dake jihar Kano

0
58
Farashin kayan masarufi a kasuwar Ɗambatta dake jihar Kano

Farashin kayan masarufi a kasuwar Ɗambatta dake jihar Kano

Daga Shafa’atu Dauda, Kano

A ziyarar da wakiliyar Neptune Prime Hausa ta kai kasuwar sayar da kayan masarufi da ke Ɗambatta ta tattauna da Sakataren ƙungiyar ma’auna ta ƙaramar hukumar Ibrahim Aminu ilu, Inda ya bayyana mana farashin kayan Masarufi a wannan Rana ta Talata 12/11/2024.

A cewar Ibrahim a wannan makon an samu hauhawar farashi sama da satin da ya gabata.

A wannan satin a na saida, buhun masara 70k, 71k. Inda a satin da ya gabata ana sai da buhun ta a kan 64k. Kwanonta ana sai dashi 1,800.

Farin Wake 116k, kwano 3k.

Alkama 116k, kwano 3k.

KU KUMA KARANTA: Farashin kayan abinci ya fara sauƙa a Najeriya

Waken suya shima an sami ƙarin farashi inda a satin da ya gabata an sai dashi 93k, 94k inda a wannan satin ake sai dashi 100,000, kwanon shi 2,600.

Dawa, 56k, kwano 1,500.

Gero 64k, kwano 1,600.

Rogo shima an sami ƙarin farashi, a satin da ya gabata an sai dashi, 55k56k.
A wannan satin kuma ya kai 65k, 70k.

Ku biyo mu sati me zuwa don jin da wace kasuwar zamu zo muku.

Leave a Reply