Farashin kayan abinci ya fara sauƙa a Najeriya

0
150
Farashin kayan abinci ya fara sauƙa a Najeriya

Farashin kayan abinci ya fara sauƙa a Najeriya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Farashin kayan abinci yana ta sauƙa a kasuwanni, sakamakon zuwan amfanin gona. Neptune Prime Hausa ta zagaya wasu daga cikin kasuwannin, don jin sabon farashin.

Alhaji Musa Mil Biyar, shi ne shugaban kasuwar Hatsi ta garin Potiskum (ɓangaren Fatake), ya shaida wa wakilinmu cewa, farashin kayan abinci ya sauƙa sosai ba kamar yadda yake a baya ba.

Sabon Gero – 53,000
Tsohon Gero – 58,000
Tsohuwar Masara – 90,000
Sabuwar Masara – 61,000
Dawa – 65,000 zuwa 70,000
Dawa – Ƙaura 80,000
Mewa – sabon farashi 100,000
Wake – 160,000 zuwa 165,000
Wake Ja – 200,000
Wake fari manya – 180,000
Gurguzun yakuwa – 31,000
Gurguzun zoɓo – 26,000.

Wannan farashin haka yake a birnin Damaturu. Amma a kasuwar Gamawan jihar Bauchi da garin Yana da Giyaɗe, ana sayar da Buhun Gero Naira dubu 60 zuwa 61.

Sabon Wake ɗan wuri Buhunsa Naira 150,000.

Shinkafa sabuwa, ‘yar ƙasa Buhunta daga 148,000 zuwa 165,000.

A kasuwar Azare kuwa ana sayar da Buhun Riɗi akan 80,000.

Alhaji Musa Mil Biyar, shugaban kasuwar Hatsi ta Potiskum

A yayin da ake sai da kwanan shinkafa sabuwa 3,900 zuwa 4,000.
Gero kwano 1,600 zuwa 1,500.

Masara sabuwa ana sayar da buhunta a kan Naira 55,000 a garin Bokkos da Mangu dake yankin Jos.

A kano kasuwar Dawanau ana sayar da masara sabuwa a kan 55,500 zuwa 56,000.

Waɗannan kaɗan kenan daga kayan da suka fara fitowa daga gona.

KU KUMA KARANTA: Rashin abinci mai gina jiki na barazana ga miliyoyin yara a Afrika.

Duk da fara sauƙa da farashin kayan abincin ya yi, amma jama’a suna koka wa da ba sa iya saya, saboda rayuwar ta yi tsada. Malam Muhammad Jalam mai Gado, ya shaida wa Neptune Prime Hausa cewa, “rashin kuɗi a hanun al’umma ya ƙaranta, ba a samun kuɗin da za a yi cefa ne.

Yanzu jama’a kowa ta abinci ya ke, ba a zuwa ma a sayi kayan namu ballantana mu samu mu yi cefa ne. Muna ga gwamnati da ta waiwayi wannan lamari don kar a jefa mutane cikin halin da ba za a iya ceto su ba”.

Malam Muhammad Jalam mai Gado Potiskum

Alhaji Babangida Manya mai Katifa, ya ce “yunwa tana ta kashe mutane. Don Allah a gaya wa Tinubu da ya dawo da tallafin man fetur ɗin nan, shi ne kaɗai hanyar da za a iya fita daga wannan ƙangin rayuwa da ake ciki”.

Leave a Reply