Farashin aure ya faɗi warwas a Gumel

0
352

Masarautar Gumel ta fitar da dokokin yin aure a sauƙaƙe.

Masarautar Gumel dake ƙaramar hukumar Gumel a Jihar Jigawa ta fitar da wasu dokoki da ƙa’idoji na aure a yankin.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata takardar sanarwa da aka fitar daga Masarautar mai ɗauke da sa hannun Alhaji Murtala Aliyu, sakataren Masarautar Gumel. Inda takardar ta nuna wasu dokoki kimanin goma sha tara da Masarautar ta ƙayyade kayan da za a yi amfani da su na aure da kuma bukukuwan aure a yankin Masarautar Gumel.

KU KUMA KARANTA: Ba zan karɓi lefe akwati 12 ba – Mahaifin wata budurwa a Kano

Ga dokokin kamar haka:

  1. Ba a ƙayyade sadaki ba amma dole ne ya dace da yanayin tattalin arziƙin al’umma.
  2. Tufafi Shida (6).
  3. Takalma uku (3).
  4. Ɗan kunne da sarƙa uku (3).
  5. Mayafi da hijabi uku (3).
  6. Ɗankwali uku (3).
  7. Kayan kwalliya seti biyu (2).
  8. Ka da kuɗin kayan lefe ya wuce Naira Dubu Ɗari (100,000).
  9. Maza ne zasu riƙa kai lefe.
  10. An hana kawo kuɗin na-gani-ina-so
  11. An hana kawo kuɗin sa rana.
  12. An hana yin gara.
  13. An hana yin kaɗe-ƙaɗen da Maza da mata za su cakuɗa da juna.
  14. Ka da shagalin biki ya wuce ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
  15. Motoci uku (3) aka yarda su kai amarya.
  16. Kai amarya ka da ya wuce ƙarfr 6:00 na yamma.
  17. An hana ƙauyawa night, Arabian night, Yoruba night da sauran su.
  18. An hana hawan angwanci sai da izinin fadar masarautar Gumel.

Leave a Reply