Falasɗinawa sun sake bijiro da buƙatar neman kujerar dindindin a MƊD ana tsaka da yaƙin Isra’ila

A hukumance yankin Falasɗinu ya sake bijiro da buƙatar neman zama mamba na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, a cewar wata wasiƙa daga wakilinsu a MDD.

“Bayan na samu umarni daga shugabannin Falasɗinawa, ina sake miƙa buƙata ga Kwamitin Tsaro a watan Afrilu na 2024 don a ba mu matsayin mamba ta dindindin,” in ji wasiƙar da Riyad Mansour ya aika wa Sakatare Janar na MƊD Antonio Guterres, wadda aka miƙa wa Kwamitin Tsaro.

Falasɗinawa, waɗanda suke matsayi na ƴan-kallo tun shekarar 2012, sun kwashe shekaru da dama suna neman a ba su matsayin mamba na dindindin, lamarin da ke nufin a amince da yankin a matsayin ƙasa mai yancin kanta, kasancewa galibin ƙasashe mambobin majalisar sun yarda ta ita a matsayin ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Falasɗinawa sun yi jana’izar mutum 28 da Isra’ila ta kashe a sansanonin ƴan gudun hijira

Masu sharhi na ganin zai yi wahala buƙatar ta Falasɗinu ta samu karɓuwa domin kuwa Amurka, babbar ƙawar Isra’ila, tana iya yin amfani da ƙarfinta a Kwamitin Tsaro don hawa kujerar na-ƙi.

Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Ƙasashe Musulmai da kuma Ƙungiyar Ƙasashe ƴan ba-ruwanmu sun aike da wasiƙa ga Sakatare Janar ma MDD ranar Talata, inda suka goyi bayan kasancewar Falasɗinu a matsayin mamba ta majalisar.

“Muna so mu jawo hankalinka cewa, a wannan ranar, mambobi 140 sun amince d kasancewar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴancin kanta,” a cewar wasiƙar haɗin-gwiwa da ƙasashen suka aika wa shugaban majalisar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *