Fafaroma Francis na ƙara samun sauƙi – Likitoci

0
269
Fafaroma Francis na ƙara samun sauƙi - Likitoci

Fafaroma Francis na ƙara samun sauƙi – Likitoci

Fafaroma Francis na ci gaba da murmurewa daga cutar pneuomonia bayan da sakamakon hoton ƙirjinsa da aka ɗauka ya nuna yana samun sauƙi.

A farkon wannan mako, likitoci sun ce rayuwarsa ba ta cikin haɗari.

Sabon rahoton likitoci ya bayyana cewa yanayin Fafaroma mai shekara 88 yana daidaita, amma an lura cewa yana fama da rashin ƙarfin jiki.

KU KUMA KARANTA:Paparoma Francis ya yi Alla-wadai da matakan Sojin Isra’ila a Gaza

A ranar Alhamis, Francis zai cika shekaru 12 da zabensa a matsayin Fafaroma na 266.

Fadar Vatican ba ta bayyana yadda za a yi bikin wannan rana ba.

A ranar Juma’a mai zuwa, Fafaroma Francis zai cika makonni hudu yana jinya a asibiti.

Leave a Reply