Faɗan daba a Kano, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da ɓarnata da dukiyoyi

0
31
Faɗan daba a Kano, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da ɓarnata da dukiyoyi

Faɗan daba a Kano, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da ɓarnata da dukiyoyin

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Unguwar Yakasai, na daga cikin wadanda kwanakin baya tayi tashe wajen gudanar da fadace-fadacen Daba, wanda Yan daban dake wannan yake suke Yar tsama da Yan badan Zage, Kofar Mata.

Wanda a wancan lokacin rigimar tafara sanya tsoro da fargaba musamman ga jama’ar dake hada-hadar kasuwa cin su a kasuwar Rimi da bakin asibitin murtala,

Dalilin hakane yasa Kwamishinan Yan sandan Kano Cp Dogo Salman Garba da Gwamnatin Kano sukayi duk wani mai yuyuwa wajen dakile wannan rigimar, wanda daga karshe Gwamnatin Kano ta gayyaci masu fadace-fadacen Daba tayi zama na musamman dasu, harma sukayi alkawarin dena wannan rigima.

Wanda al’ummar wannan yankuna suka sami salama, dama masu hada-hadar kasuwa cin a wannan yankuna, yanzu kuwa a iya cewa murna ta koma ciki sakamakon bakin jiya sun dawo.

KU KUMA KARANTA:Sace wayoyin da aka binne kusa da fadar shugaban ƙasa ya jefa unguwannin Abuja cikin duhu -TCN

Mazauna unguwar ta yakasai, masallacin jalli, kankarofi, da batakulki, da kasuwar rimi sun shaida cewa an fara fadan dabar tin da misalin Ƙarfe 10:20 na dare yayin da aka kai har lokacin sallar asuba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kwana uku Kenan ana tafka fadan a cikin waɗannan lokuna har izuwa yanzu an kasa kawo karshen faɗan dabar.

Munyi duk mai yiyuwa dan jin ta bakin masu unguwannin yankin amma har izuwa yanzu hakan bata Samu ba

Wani mazaunin Kankarofi yace Yana Sama Yan dabar suka fara sai dukkanin su sun ɓoye fuskarsu abin jira a gani irin matakin da mahukunta zasu ɗauka.

Leave a Reply