eNaira: CBN ya gayyaci wani kamfani na Amurka domin gyara lamarin– Rahoto

0
257

Domin samar da ingantaccen kuɗin dijital da kuma tabbatar da karɓuwar jama’a, Babban Bankin Najeriya ya tuntuɓi wani kamfanin fasaha na New York don saɓunta fasahar da ke cikinsa.

A cewar rahoton Bloomberg, CBN na tattaunawa da sabbin ‘abokan fasaha’ don samar da wani sabon tsari da ingantaccen tsarin sarrafa eNaira.

An ba da rahoton cewa babban bankin ya tattauna tsare-tsaren tare da kamfanin fasaha na New York, R3. Rahoton ya yi iƙirarin cewa za a ƙirƙiri sabuwar manhaja ta eNaria ne domin ba da damar CBN ya sami cikakken iko akan shirin.

An kuma lura da cewa an fara yunkurin samar da eNaira ne a shekarar 2021 tare da taimakon kamfanin sarrafa kayan masarufi, Bitt. Rahoton ya bayyana cewa sabon abokin tarayya ba zai ɗauki aikin Bitt nan da nan ba amma zai taimaka wajen sarrafa gaba ɗaya ga babban bankin ƙasar.

Da take mayar da martani game da hakan, Bitt ta ce tana sane da cewa CBN na aiki da abokan hulɗa daban-daban domin samar da sabbin fasahohi. Ya tabbatar da cewa har yanzu yana aiki kafaɗa da kafaɗa da CBN kuma “a halin yanzu yana haɓaka ƙarin fasali da haɓakawa.”

KU KUMA KARANTA: CBN zai hukunta duk bankunan da ke ɓoye sabbin kuɗi

Duk da cewa yana ɗaya daga cikin kasashen farko da suka kaddamar da kuɗin dijital na Babban Bankin Najeriya, eNaira ta Najeriya ta fara tafiya a hankali, tare da karancin karbuwa.

Tun tun bayan ƙaddamar da shi a shekarar 2021, amfani da eNaira, kuɗin dijital na Najeriya, ya kasa karɓa, a cewar asusun lamuni na duniya.

A cewar asusun, kusan kashi takwas cikin 100 na wallet na eNaira ne ake amfani da su, inda aka samu matsakaitan ciniki na N53,000. Ya bayyana cewa ya zuwa watan Nuwamba 2022, jimillar zazzagewar jakar eNaira ya kai 942,000.

Leave a Reply