El-Rufai ya bar wa jihar Kaduna ɗimbim bashi – Gwamnan Uba Sani

0
185

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamna Uba Sani ya bayyana haka ne a Kaduna a ranar Asabar yayin da yake jawabi a wajen wani babban taron ji daga jama’a, inda ya ce ɗimbim bashin da ake bin jihar Kaduna shi ke laƙume ɗan abin da ta ke samu.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta gaji bashin Dalar Amurka Miliyan 587 da bashin Naira Biliyan 85 da kuma ayyukan kwangila 115 daga gwamnatin Nasir El-Rufai.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira Biliyan 7 daga cikin Naira Billiyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata a watan Maris, domin biyan bashi.

Gwamnan ya kuma koka kan tashin farashin canji, wanda ya ce jihar na biyan kusan ninki uku na bashin da gwamnatin baya ta karɓo.

KU KUMA KARANTA: Nijar ta gaza biyan bashin da ya kai dala miliyan ɗari biyar – WAEMU

Ya Kuma koka da yadda gwamnatin El-Rufai ta bar wa jihar Biliyan uku kacal a asusun, wanda ya gaza biyan albashin ma’aikata da ake biya na Naira Biliyan 5.2 a duk wata.

Gwamnan ya ƙara da cewa muhimman abubuwan da gwamnatin sa ta sa a gaba sun haɗa da tsaro, samar da gidaje, ilimi, kiwon lafiya da tallafa wa masu ƙananan sana’o’i.

Ya ce gwamnatin sa za ta kuma mayar da hankali wajen samar da ci gaba ta hanyar saka hannun jari, inganta tattalin arziƙi da samar da gidaje masu sauƙi.

Ya ka bayyana wasu muhimman abubuwan da gwamnatin tasa ta sa a gaba a 2024 da suka haɗa da tsaro, samar da ababen more rayuwa, bunƙasa ilimi, samar da gidaje da ci gaban birane da dai sauransu.

Leave a Reply