ECOWAS za ta janye harajin da ta kakaɓa wa wasu ƙasashe
Shugabannin Ƙungiyar Ƙasashen ECOWAS sun tsaida shawarar ragewa ko kuma janye harajin da aka kakaɓawa waɗansu ƙasashe da su ka shafi tafiye-tafiye ko kuma shigar da kaya.
Shugabannin na kungiyar ECOWAS sun tsaida wannan yarjejeniyar ne a taron da su ka gudanar a Abuja.
Wannan matakin ya shafi batun cire haraji a kan kaya da ake shigowa da su daga waɗansu ƙasashen da ke cikin ƙungiyar, da haraji kan tikitin jirgi domin ya yi sauki, da bututu wanda zai ɗauki iskar gas daga Najeriya ya bi ta dukan waɗannan ƙasashen, da kuma Najeriya da Morocco.
KU KUMA KARANTA: Ƙofofin ECOWAS a buɗe suke ga ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso ; Tinubu
Masu kula da lamura sun bayyana cewa, wannan matakin da ƙungiyar ECOWAS ta dauka zai taimaka gaya wajen buƙasa tattalin arzikin ƙasashen, ya kuma rage tsadar rayuwa da talauci da galibin ƙasashen ke fama da shi.