Ecowas za ta gudanar da taron ƙoli kan Nijar a Abuja

1
255

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar ƙasasahen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO, ta ce za ta gudanar da taron ƙoli a babban birnin Najeriya, Abuja a ranar Alhamis domin tattauna batun Nijar, inda aka yi juyin mulki.

Wakilin BBC ya ce, a ranar Lahadi jagororin juyin mulkin suka yi watsi da wa’adin da ECOWAS ta ba su na su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki, ko kuma su fuskanci matakin soji.

Ƙasahen Burkina Faso da Mali sun ce za su tura tawagar haɗin gwiwa domin nuna goyon baya zuwa Nijar.

1 COMMENT

Leave a Reply