Connect with us

Labarai

ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro – Badaru

Published

on

ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro - Badaru

ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro – Badaru

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS tana buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don samar da ƙaƙƙarfar rundunar tsaro da za ta yi yaƙi da ta’addanci, a cewar ɗaya daga cikin zaɓuka biyun da hukumomin tsaro na ƙasashen yankin ke duba yiwuwarsu a taron da suka yi a jiya Alhamis.

Ministocin Tsaro da na Kuɗi na Ƙasashen ECOWAS sun yi taron a Abuja, babban birnin Najeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da kuma yawan kuɗaɗen da ake buƙata don samar da ita.

Afirka ta Yamma na fama da matsalolin juyin mulki, lamarin da yake zama matsala ga tsarin siyasa da jawo rarrabuwar kai tsakanin ƙasashen yankin.

KU KUMA KARANTA: Masana sun yi ƙira da a yi sabbin sauye-sauye ECOWAS

A watan Janairu, shugabannin mulkin soji na Nijar da Burkina Faso da Mali sun yanke shawarar ficewa daga ƙungiyar mai mambobin ƙasashe 15.

Ministan Tsaron Najeriya ya shaida wa taron cewa akwai zaɓi biyu a samar da rundunar yankin: Daya za a kashe dala biliyan 2.6 duk shekara a kan runduna mai dakaru 5,000, dayan kuma za a kashe dala miliyan 481 a dakaru 1,500
“Waɗannan alkaluma sun nuna muhimmancin aikin da ke gabanmu,” in ji Badaru.
“Don haka ya zama wajibi mu yi nazari sosai kan zabin duba da irin kalubalen da yankinmu ke fuskanta a halin yanzu da kuma matsalolin kudi da kasashe mambobinmu ke fuskanta.”

Tun a shekarar 2020, sojoji a kasashen uku suka yi juyin mulki suna zargin shugabannin farar hula da ƙyale masu da’awar jihadi su samu galaba.

Da hawansu kan mulki, sojojin sun yi watsi da yarjejeniyoyin tsaro da aka ƙulla da sojojin Amurka da Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya tare da gayyatar Rasha da su maye gurbinsu.

Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ɗaukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai yaƙi da ta’addanci. Ana sa ran kowace ƙasa mamba za ta ba da gudunmawar wani kaso, in ji shi.

Shugaban hukumar ECOWAS Omar Touray ya ce ba za a cire mambobin da aka dakatar daga cikin rundunar yankin ba.

“An yi imanin ba za mu iya yaki da ta’addanci mu kadai idan har wasu ba su shiga ba,” in ji Touray.

“Ko da yake ana iya dakatar da wasu kasashe amma ya kamata a bar su su shiga tarukan da suka shafi tsaro, shi ya sa muka gayyaci dukkan kasashe mambobi 15 da su halarci wannan muhimmin taro.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like