Duk wanda taka doka a bukukuwan Sallah, doka za ta yi aiki a kansa – Hukumar tace Fina-Finai ta Kano

0
240
Duk wanda taka doka a bukukuwan Sallah, doka za ta yi aiki a kansa - Hukumar tace Fina-Finai ta Kano

Duk wanda taka doka a bukukuwan Sallah, doka za ta yi aiki a kansa – Hukumar tace Fina-Finai ta Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ba za mu saurarawa duk wani gidan wasa ba idan ya sauka daga turbar addini ko al’adar Hausawa ba, a lokacin shagulgulan bikin ƙaramar sallah.

Zamu hukunta duk wani Gidan wasa da yabar masu shigar banza Ko ya hada maza da mata ko masu shaye-shaye a cikinsa a yayin shagulgulan bikin Karamar sallah

A kokarin ta na yaki da rashin da’a tare tsaftace yadda gidan wasanni da masu kidan DJ zasu gudanar da shagalin bikin sallah a Jahar Kano, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin shugabanta Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka kafar wando daya da duk wani gidan wasa ko mai kidan DJ aka samu da aikata yin rashin da’a a yayin gudanar da bikin sallah a Jahar Kano, inda Hukumar tace ta shirya wata tawaga ta musamman da zasu kewaya gidajen wasannin a ranakun sallah karkashin kulawar Alh. Abubakar Zakari Garun babba Daraktan Dab’i na Hukumar.

KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai a Kano ta kama matashi da budurwar da suke baɗala a soshiyal midiya

Tawagar wacce aikinta shine saka ido akan dukkannin gidajen wasannin a fadin Jahar hadi da masu kidan DJ zasu tabbatar ba’a bawa masu shigar banza ko shaye – shaye damar shiga gidajen wasannin ba haka kuma,

Haka zaluka Hukumar ta hana hada maza da mata a guri daya a yayin bikin sallar. Abba El-mustapha yace tawagar zasu rinka aiki ne babu dare ba rana a cikin sirri tare da bayyane tun a rana daya ga sallah har zuwa lokacin da za’a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da akasa a gaba.

Abba El-mustapha na Kara yin gargadi da kakkausar murya ga masu gidajen wasanni tare da masu sana’ar DJ dasu bi dokokin Hukumar sau da kafa domin gujewa fushin Hukumar. A karshe ya yi kira da iyaye dasu cigaba da kula da tarbiyar ya’yansu tare da addu’ar Allah yasa ayi bikin na sallah lafiya a gama lafiya

Leave a Reply