DSS ta gargaɗi ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya a kan shirin zanga-zangar ‘tsadar rayuwa’

0
158

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar da take yi a ƙasar “don guje wa jawo tashin hankali da hargitsi.”

A sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, DSS ta ce duk da cewa hukumar ƙungiyar ƙwadago na da damar shirya hakan bisa kundin tsarin mulki, tana ganin “bin tsarin tattaunawa zai fi kamata maimakon yin abin da zai tayar da hankula.”

Tun da fari Ƙungiyar Ƙwadago ta sanar da shirya yin zanga-zangar a ranar Alhamis da nufi nuna takaicinsu kan halin matsi da tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya.

“Hukumar DSS tana sane da cewa wasu ɓata gari suna shirin amfani da zanga-zangar don ƙirƙirar rikici da jawo tashin hankali,” ta faɗa a sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.

Ta ce a ganinta babu abin da zanga-zangar za ta yi sai ƙara ta’azzara yanayin zamantakewar tattalin arziki da ake ciki a faɗin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Sheikh Muhajjadina ya nemi gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki kan tsadar rayuwa

Hukumar ta yi jan hankali da cewa “a bayyane yake cewa dukkan sassan gwamnati suna ƙoƙarin magance matsalar tattalin arzikin da ake ciki, kuma bai kamata a raina ƙoƙarinsu ba.”

A ƙarshe DSS ta jawo hankalin ƴan ƙasa da su guji shiga zanga-zangar, tana mai cewa “abin da haƙuri bai samar ba, rashin haƙuri ba zai samar da shi ba.”

Leave a Reply