Wani direba da ake zargi da take ma’aikatan shara har lahira a lokacin da suke tsaka da aiki a Legas ya miƙa kansa ga hukuma.
Ana zargin zargin direban ya yi ajalin masu sharan ne bayan da ya taho a guje inda ya kaɗe su a lokacin da suke tsaka da aikinsu a gefen babban titin Gbagada a ranar Litinin.
Kakakin ’yan sanda a jihar, Benjamin Huneyin, ya tabbatar cewa direban da ya miƙa kansa ga rundunar yana nan a hannunsu.
Amma jami’in ya ce “ abun da ya faru ba kisa ba ne haɗari ne, kuma za mu gurfanar da shi gaban kotu bisa zargin kisan kai, amma ba na ganganci ba”.
KU KUMA KARANTA: Ya kashe direba don ya ajiye mota a inda aka hana – ‘Yan sanda
A baya dai an ruwaito cewa, direban ya kaɗe ma’aikatan sharar su biyu, suka mutu nan take, shi kuma ya tsere ya bar motar sa a wajen da abin ya faru.
Ana zargin hakan ta faru ne a bayan ya taho a guje da nufin tsere wa jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar, waɗanda suka biyo shi a baya.
Sai dai ma’aikatar sufiri ta jihar ta ce babu wani jami’in ta da ke da hannu a faruwar al’amarin, ‘amma bayan binciken ’yan sanda, idan akwai ma’aikacinmu da ke da hannu za mu hukunta shi daidai da yadda doka ta ce.’