Dalilin da ya sa mu ka sake ƙara farashin man fetur — NNPC
Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya kare matakin da ya ɗauka na ƙara kuɗin man fetur a karo na biyu cikin wata guda.
Lawal Sade, shugaban NNPCL sashen kasuwanci da cinikayya na kamfanin ya ce hakan ta faru ne saboda yanayin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma yanayin canjin kuɗin waje.
KU KUMA KARANTA:Ba mu muka ƙara farashin man fetur ba — Gwamnatin Tarayya
Sai dai ya ce NNPCL na wa ‘yan Najeriya albishir cewa farashin zai iya saukowa idan sauran matatun mai na cikin gida suka fara aiki gadan-gadan.
BBC Hausa ta rawaito cewa Sade ya kuma nemi afuwar ‘yan Najeriya game da matakin ƙarin.