Dalilin da ya sa aka dakatar da Sheikh Bin Uthman daga limancin masallacin Sahaba
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a da ake kira da Masjid Sahaba, ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga limanci biyo bayan huɗubar da ya yi a ranar 24 ga watan Janairu.
Asalin masallacin, wanda Bin Uthman ke jagoranta tsawon shekaru 24, na kusa da sabon wanda AY Maikifi ya sayi filin.
Bayan Maikifi ya samu mallakar filin a hannun gwamnati don gina sabon masallacin Sahaba, sai ya tuntubi Bin Uthman inda suka amince da cewa tshohon masallacin Sahaba zai dawo sabon gini.
Sai dai kuma a yayin huɗubar da ya yi a ranar 24 ga watan Janairu, wacce ta haifar cece-ku-ce, Bin Uthman ya ba da labarin yadda aka rage masa matsayi wajen gudanar da harkokin masallacin.
A cewar sa, an naɗa shugabanni uku masallacin amma ba a naɗa shi a jagora ba.
KU KUMA KARANTA:An gudanar da taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 49 a Bauchi
Huɗubar ta ranar 24 ga watan Janairu ta fusata masallata, inda suka kusa dukan sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Abdulkadir Isawa.
Hukumar kula da masallacin, a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun daraktan gudanarwa, ta dakatar da Bin Uthman har sai baba-ta-gani, tare da umartar shi da ya mika dukkan kayan masallacin da ke hannunsa.
A ranar Litinin din data gabata ne kuma hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, da majalisar malamai suka gayyaci Malam Bin Usman da wanda ya assasa sabon masallacin, Maikifi.
Hukumar SSS, a cewar majiyoyi, ta gargadi Bin Uthman kan huɗubar da su ka ce ka iya haifar da rikici ko hari a cikin masallacin.