0
14
Dalilin da ya sa aka ɗage taron 'Qur’anic Convention' a Abuja

Dalilin da ya sa aka ɗage taron ‘Qur’anic Convention’ a Abuja

Wannan na ƙunshe a sanarwa da sa hannun babban sakataren majalisar Farfesa Ishaq Oloyede da ke bayyana dage taron, wanda tun farko a ka shirya gudanarwa a ranar 22 ga watan nan na Febrairu na wannan shekara.

Wakilin Muryar Amurka ya ce ya kai ziyara sakatariyar taron inda ya tarar ana bitar alarammomi da ke shirin tahowa, amma dakatarwar ta sa jan birki don sake sabon shiri sakamakon wuce adadin da ake sa ran za su zo da fiye da kashi 400 cikin 100.

Shugaban sakatariyar, Malam Bala Isa Alfa, ya ce majalisar kolin da manyan malamai na kungiyoyin musulunci da ke shirya taron sun dau matsayar a bi jerin sunayen a tsanake don zama a rukunu-rukuni da zummar gujewa abun da ya zaiyana da turereniya.

Ya ce kalubalen tsare-tsare ne suka samu dage taron don an zarta adadin daga mutum dubu 30,000 zuwa fiye da mutum dubu 500,000 da suka yi rajista.

Da yake amsa tambaya kan anya ba yawan sukar taron ne ya sa daukar matakin ba? Malam Bala Isa ya ce “sukan ba zai hana su abun da su ke so su aiwatar ba, sai ma sukan ya zaburar da su ne don su samu kyakkyawan shiri.”

KU KUMA KARANTA:An kammala shirin taron ‘Qur’an Convention’ a Abuja

Tarot dai hakika na da goyon bayan kusan dukkan shahararrun malaman Islama, amma akwai wasu da ke cewa hakan ba shi ne abun da mahaddatan ke bukata, inda wasu kuma na cewa ba shi da asali a tarihin Islama.

Idan za’a tuna babban Shehun Malamin Islama, Shariff Ibrahim Saleh Al-Hussaini, ya ce ba laifi ba ne mutane su taru su karanta Al-kur’ani ko su taimaki juna duk da kuma ba shi kadai ba ne aikin alheri da ake sa ran al’umma ta aikata.

Yanzu haka an shiga muhawara a yanar gizo tsakanin masu fatan alheri ga taron da masu hamayya da shi da sakatariyar ke fatan kowa zai fahimci alherin shirin.

Hakika dawainiya ce a ga manyan bakin da aka gayyata da su ka hada da babban limamin haramin Makkah Dakta Abdulrahman Sudai su halarci taron da zai gudana kafin dagewa mako daya kafin fara azumi.

Leave a Reply