Dalilin da ya sa Ahmed Musa bai buga wasa ko ɗaya ba, a wasan cin kofin Afirka

0
189

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kocin Super Eagles Jose Peseiro ya magantu kan damuwar da ‘yan Najeriya ke nunawa ta rashin buga wasa da kyaftin ɗin tawagar Ahmed Musa ke fama da shi.

Ahmed bai buga ko wasa guda ba cikin huɗu da suka buga a gasar Afcon da ke gudana a Côte d’Ivoire ta 2023.

Amma kocin ya ce duk da rashin buga wasan da Ahmed ke yi yana da amfani a cikin tawagar.

Sai dai kocin ya ce “Ko a benci Ahmed Musa na mana amfani”

“Zai iya buga wasa, amma abin da mutane ya kamata su sani shi shugaba ne,” kamar yadda Peseiro ya bayyana a taron manema labarai da ake yi idan an kammala wasa.

Ya jadda cewa zaman Musa a benci shi kan shi wata dama ce ta musamman ga matasan ‘yan wasan tawagar, tun da suna yi masa kallon abin koyi.

KU KUMA KARANTA: CAF za ta yi bincike kan rikicin da ya faru bayan wasan Maroko da DRC a gasar AFCON

“Gudunmuwarsa ta kasu kashi biyu, ta cikin fili da kuma ta waje. Idan ba shi da amfani da ba mu ƙira shi ba tun da fari,” in ji kocin.

Leave a Reply