Dalilin bayyanar jami’an tsaro da yawa a Jigawa – ‘Yan Sanda

1
1448

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa an ga yawan manyan jami’an tsaro a Jigawa ne domin daƙile rashin zaman lafiya a zaɓen da za a sake gudanarwa a ranar Asabar.

A cewar kwamishinan ‘yan sanda, Effiom Ekot, lamarin ba shi da alaƙa da fashewar wani abu da ya faru ranar Talata a Dutse inda mutum ɗaya ya jikkata.

Mista Ekot ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai gabanin sake zaɓen majalisar a ƙananan hukumomi biyar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wata na’ura ta fashe a babban titin Hakimi dake Dutse inda wani ɗan kasuwa mai suna Friday Frayo ya jikkata.

KU KUMA KARANTA: An kori ‘yan sandan dake tsaron Rarara saboda wasa da alburusai

Tun daga wancan lokaci, shingayen binciken sojoji suka ɓulla a kan manyan hanyoyin jihar. “Muna so mu wayar da kan al’ummarmu kan harkar tsaro tare da gaya wa masu son kawo rikici a jihar su sani cewa muna nan a ƙasa kuma ba za mu amince da duk wani yanayi da zai haifar da fargaba ba.

“Ina so in yi ƙira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu. Haɓaka ganin ‘yan sanda da sojoji don zaman lafiya da alherin mu duka ne.

“Don haka ya kamata mutane su ba da haɗin kai da dukkan hukumomin tsaro don tabbatar da cewa jihar ta ci gaba da riƙe matsayinta na jiha ta ɗaya a kasar,” in ji kwamishinan

Ya ba da tabbacin cewa “babu wanda ake tursasawa kuma babu wanda za a musgunawa. Masu yin sana’o’insu na halal su ci gaba da yin hakan ba tare da wata fargaba ba.

“Batun binciken ba saboda fashewar kwanan nan ba ne, amma don zaɓen gobe, don haka ka da masu yin kasuwancin halal su ji tsoro.”

Shugaban ‘yan sandan ya bayar da tabbacin cewa, ana gudanar da bincike a kan fashe-fashen, inda ya ƙara da cewa duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin, za a hukunta shi.

Sai dai ya ce babu wani kama da rundunar ta yi, amma ya ƙara da cewa ‘yan sanda na kan gaba wajen lamarin.

A halin da ake ciki, Mista Ekot ya yi wata ganawa da shugabannin addini da su ja kunnen mabiyansu da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wani fuska ko motsi da suka samu ga hukumomin tsaro.

Ya kuma shawarce su da su ɗauki matakan kariya a wuraren ibada da suka haɗa da tantance masu ibada.

1 COMMENT

Leave a Reply