Dakarun tsaro a Borno sun daƙile wani harin Boko Haram

0
28
Dakarun tsaro a Borno sun daƙile wani harin Boko Haram

Dakarun tsaro a Borno sun daƙile wani harin Boko Haram

Wasu dakarun tsaro na rundunar haɗin-gwiwa ta ƙasashe, wato MNJTF, wadda ke aiki ƙarƙashin shiyya ta 3 da aka girke a Jihar Borno ta samu nasarar daƙile wani harin ‘yan Boko Haram a jihar da take arewa masu gabashin Najeriya.

Babban jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin ta MNJTF wadda ke birnin N’djamena, na Chadi, Lieutenant Colonel Olaniyi Osoba ya sanar da haka a wata sanarwa ranar Lahadi.

Jami’in ya ce dakarun sun yi aiki da wasu bayanan sirri da suka samu, inda suka ƙaddamar da wani kwanton ɓauna, kuma suka daƙile barazanar tsaro daga ‘yan ta’adda da suka so afkawa farar-hula.

“Dakarun sun yi dakon hanyar da ‘yan ta’addar suke wucewa, inda suka far musu yayin da suke fitowa daga daji kan babura, ta wata hanya da da ba a saba bi ba,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe yan ta’adda 159 a mako guda – Hedikwatar tsaro

“Suna ganin dakarunmu, ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin arcewa amma sai aka musu ɓarin wuta. Wannan gagarumin farmaki ya tilasta musu barin makamansu da baburansu, wanda ya katse shirinsu na ƙaddamar da hari kan yankin.

“Bayan ƙazamin faɗa, dakarun sun karaɗe yankin kuma sun kwaso tarin makamai da suka haɗa da AK-47 2, da alburushi na musamman 51 masu girman 7.62mm, da jigidar alburushi biyu, da alburushi samfurin 7.62 na NATO guda 61, da sauran abubuwa, ciki har da wiwi, da Tramadol, da sigari.

“Wannan matakin gaggawar da dakarun rundunar MNJTF suka ɗauka ya kawar da harin da ka iya afkuwa kan al’umma, tare da ƙarfafa matakan da ake ɗauka don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin tafkin Chadi.”

A cewar Osoba, matakin ya nuna yadda rundunar tsaron take shan alwashin samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da ke ƙarƙashin kulawarta.

Ya ƙara da cewa dakarun sun tsananta shawagin da suke a gabaɗaya yankin don kaucewa sake faruwar hare-haren ‘yan ta’adda, wanda ke nuni da shirinsu na kawar da duk wata barazana da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Leave a Reply