Hukumar sojin Najeriya ta ƙara tono ababen fashewa a wurin da bam ya tashi shekaru 21 da watanni tara da suka gabata a Ikeja, babban birnin jihar Legas.
Hukumar sojin ƙasa ta Najerriya ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya.
Tashin bama-baman wanda ya auku ranar 27 ga watan Janairu, 2002 a sansanin sojoji da ke Ikeja, ana kyautata zaton ya halaka mutane aƙalla 1,100 yayin da wasu sama da 20,000 suka rasa mahallansu.
Bayan haka tashin bama-baman ya jikkata dubbannin mutane tare da jefa wazu da dama cikin halin ƙaƙanikayi.
An ce Bama-bamai da wasu ababen fashewa sun tashi ne bisa kuskure a cikin sashin ajiye makamai na barikin sojoji sama da shekaru 21 da suka wuce.
KU KUMA KARANTA: Sojin ruwa ta kama kwale-kwale ɗauke da muggan ƙwayoyin naira miliyan 200
Fashewar wadda ta yi ƙara kusan sau bakwai, cikin kwanaki biyu, ta yi sanadin lalata dukiyoyi a yankin da kewaye. Lamarin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi.
Da yake jawabi a Legas ranar Talata yayin ƙaddamar da shirin tsaftace wurin, babban Hafsan Sojojin ƙasa (COAS), Laftanar-Janar Tajudeen Lagbaja, ya ce a ƙarshe rundunar aikin kwashe abinda ya rage.
COAS ya bayyana cewa rundunar soji ta fara jigilar sauran bama-bamai da ababen fashewar da ba su fashe ba a wancan lokacin zuwa ɗaya daga cikin sansanonin ta da ke Ajilete, jihar Ogun.
Ya ce aikin share da tsaftace wurin na farko da aka yi a shekarar 2002 ya ƙara tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin Ikeja da kewaye.
Lagbaja ya ƙara da cewa sun gano wasu bama-bamai da ba su fashe ba a wurin da ibtila’in ya faru kuma hakan ne ya nuna akwai buƙatar sake tsaftace wurin a yanzu.
“Ina ƙara tabbatar wa ‘yan Najeriya musamman mazauna Legas da Ogun cewa za a gudanar da wannan aiki cikin ƙwarewa da kuma taka tsantsan da bin matakan da ya dace.”