Daga fara Azumin Ramadan, mutane 11 ne suka musulunta a wajen tafsirin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

0
16
Daga fara Azumin Ramadan, mutane 11 ne suka musulunta a wajen tafsirin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Daga fara Azumin Ramadan, mutane 11 ne suka musulunta a wajen tafsirin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Fitaccen malamin addinin muslunci a Kano, kuma kwamanandan Hisbah Al-Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa, ya samu gagarumin nasara daga farkon watan Ramadan zuwa yanzu.

Wanda ya musluntar da mutum 11 a wurin tafseer din sa, malamin ya bayyana jindadinsa bisa wannan gagarumin nasara da Allah yaba shi.

Wanda yace tuni wadanda suka karbi kalmar shahadar suka zabi sunayen da suke so kamar haka.

1. Hauwa
2. Jamila Usman
3. Fatima
4. Yakubu Abdullahi
5. Fatima
6. Aisha
7. Daud
8. Muhammad
9. Fatima
10. Hafsat
11. Fatima

KU KUMA KARANTA:Ba za mu sauya tsarinmu na rufe makarantu a watan Azumi ba – Gwamnonin Kano, Bauchi, da Kebbi

Kuma Malam yayi bayanin cewa daga yanzu an dena haska wadanda suka karbi muslunci a na’urar Camera, sakamakon wasu suna musu barazana,

Shiyasa aka kawo sabon tsari da zai tsare musu lafiyarsu dama rayukansu.

A karshe malam ya yi kira ga al’ummar muslumi wajen cigaba da rungumar zaman lafiya.

Leave a Reply