Cutar Lassa: Gwamnatin Kano za ta kashe Ɓerayen ƙaramar hukumar Garun Malam

0
173
Cutar Lassa: Gwamnatin Kano za ta kashe Ɓerayen ƙaramar hukumar Garun Malam

Cutar Lassa: Gwamnatin Kano za ta kashe Ɓerayen ƙaramar hukumar Garun Malam

Daga Shafa’atu Dauda Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta dauki matakin kashe Ɓeraye, a karamar hukumar Garun Malam domin dakile yaduwar cutar Lassa.

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar, Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa, ya aiko wa jaridar NEPTUNE PRIME Hausa a yammacin jiya Alhamis inda ya ce ya zama dole gwamnati ta dauki wannan mataki cikin gaggawa domin kare lafiyar al’umma, ganin yadda aka tabbatar da bullar cutar Lassa a Garun Malam, wacce ta yi sanadin rasuwar wata baiwar Allah.

KU KUMA KARANTA:Cutar Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Kwamishinan ya bayyana cewa tuni aka killace duk wadanda suka yi mu’amala da mamaciyar, ciki har da mijinta da kuma jami’an lafiyar da suka kula da ita lokacin da aka kawo ta asibiti, wanda kuma binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mijin marigayiyar da daya daga cikin yaranta sun kamu da cutar.

Dakta Labaran ya kuma jaddada cewa kashe Ɓerayen da ke yankin da abin ya shafa wani muhimmin mataki ne na dakile yaduwar cutar, kasancewar Ɓeraye na daga cikin manyan hanyoyin yada cutar Lassa.

Gwamnatin ta kuma ja hankalin mafarauta da su guji farautar Ɓeraye, da kuma daukar matakan kariya domin hana yaduwar cutar daga jikinsu zuwa mutane.

A karshe Kwamishinan ya shawarci jama’a da su rika hanzarin sanar da jami’an lafiya mafi kusa idan suna zargin wani da cutar Lassa, haka zalika ya bukaci jami’an lafiya da su dauki matakan kariya yayin da suke kula da masu fama da cutar, domin kauce wa yaduwar ta

Leave a Reply