COAS ya yi kira ga sabbin sojojin Najeriya 3,439 kan ladabi, aminci da ƙwarewa
Daga Idris Umar, Zaria
Babban Hafsan Sojin Kasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi kira ga sabbin sojojin Najeriya 3,439 da aka kammala horaswa da su riƙe mafi girman matakai na aminci, ladabi da kwarewa yayin da suka shiga aikin soja a hukumance.
Sabbin sojojin, mambobin Kashi na 89 na Daukar Ma’aikata na Rundunar Sojin Najeriya, sun kammala watanni shida na tsauraran horaswa a Depot Nigerian Army, Zariya, Jihar Kaduna. An gabatar da su a hukumance a Rundunar Sojin Kasa yayin bikin Passing Out Parade da aka gudanar a Zariya
COAS ya bayyana faretin a matsayin “shaida ta jajircewa da dagewa,” inda ya ce bikin ya nuna ladabi, kwarewa da ruhin haɗin kai (esprit de corps) da aka gina a zukatan sabbin sojojin tsawon lokacin horaswar.
Yayin jawabi a matsayin Bako na Musamman kuma Mai Duba Fareti, Laftanar Janar Shaibu ya ce kammala horaswar cikin nasara alama ce ta aiki tukuru, jajircewa da ladabi.
“Nasarar kammala horaswarku ta nuna aiki tukuru, jajircewa da ladabi. An gina ku bisa mafi girman ka’idojin aikin soja, kuma yanzu an dora muku nauyin tsarkakakken aikin kare cikakken ikon ƙasar mu,” in ji shi.

Babban Hafsan Sojin ya jaddada muhimmancin karin ma’aikata wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, yana mai cewa Rundunar Sojin Najeriya na fuskantar sabbin barazanar tsaro na cikin gida da na ketare.
“Ba ni da shakka cewa za ku tashi tsaye wajen fuskantar kalubalen da ke gaba, ku yi aiki da mutunci, jarumtaka da kwarewa. Shigarku a yau ba kawai ƙarin sojoji ba ne, har ila yau ƙarfafa ƙudirinmu na tabbatar da tsaro da zaman lafiyar kowane ɗan Najeriya,” ya ƙara da cewa.
Laftanar Janar Shaibu ya bayyana Rundunar Sojin Najeriya a matsayin runduna mai ƙwarewa kuma shirye-shiryen yaƙi, wadda ke da ikon mayar da martani cikin gaggawa ga duk wata barazana ga ƙasa.
KU KUMA KARANTA: Dole sojojin Najeriya su koyi harsunan gida don samun sahihan bayanan sirri — COAS
Ya yaba wa Depot Nigerian Army bisa rawar da take takawa tun kafuwarta a 1924 wajen samar da ƙwararrun sojoji, yana mai cewa cibiyar ita ce ginshiƙin tsarin horaswar Rundunar Sojin Najeriya.
“Ina tabbatar muku da cewa za a ci gaba da ba ta cikakken goyon baya ta fuskar kayan aiki, inganta wuraren horaswa da walwalar ma’aikata domin kiyaye kyawawan ka’idojinta,” in ji shi.
COAS ya kuma shawarci sabbin sojojin da su ci gaba da kiyaye ladabi, gaskiya da mutunta haƙƙin bil’adama a dukkan ayyukansu, yana mai jaddada cewa waɗannan su ne tubalin aikin soja na ƙwarai.
Dangane da Rantsuwar Aminci da suka yi, ya ce: “Ta wannan rantsuwa, yanzu kun ɗaure kanku wajen bin dokokin farar hula da na soja. Ku guji duk wani abu da zai iya bata sunan Rundunar Sojin Najeriya ko ƙasar mu. Ku yi aiki da mutunci, daraja da cikakken biyayya ga halattacciyar hukuma.”
Laftanar Janar Shaibu ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da sauran hukumomin tsaro bisa ci gaba da ba Rundunar Sojin Najeriya goyon baya.
Ya kuma yaba wa Kwamandan Depot Nigerian Army, malamai masu horaswa da sauran ma’aikata bisa jajircewarsu wajen samar da ƙwararrun sojoji.
“Barka da kammala horaswa ga sabbin sojojin da suka fito, iyayensu da masu kula da su bisa wannan gagarumar nasara. Allah Ya sanya ayyukanku su zama masu ɗaukaka, hidimarku abin koyi, kuma tura ku zuwa sassan rundunar cikin aminci da albarka,”









