China da Vietnam sun dawo da danƙon zumunci a tsakaninsu, bayan takun saƙa a baya

0
42
China da Vietnam sun dawo da danƙon zumunci a tsakaninsu, bayan takun saƙa a baya

China da Vietnam sun dawo da danƙon zumunci a tsakaninsu, bayan takun saƙa a baya

A ranar Asabar Gwamnatin Vietnam ta ce, sun amince ita da China su ƙarfafa haɗin guiwa domin bunƙasa sha’anin tsaro da kare kansu, duk kuwa da lokacin da suka ɗauka suna ‘yar tsama da juna kan batun kogin kudancin China.

China ce dai abokiyar hulɗar kasuwanci mafi girma ga Vietnam, kuma babbar kafar da take shiga da kayayyakin sarrafawa a masa’antu cikin ƙasar ta.

Hakazalika ƙasashen biyu, sun amince a ranar Asabar su bunƙasa hulɗar tattalin arziƙi a tsakanin su, inda China ta sha alwashin ƙara buɗe ƙofar kasuwannin ta ga kayayyakin amfanin gonar ƙasar ta Vietnam, yayin da ita kuma Vietnam ɗin za ta bunƙasa zuba hannun jarin ta a China, kamar yadda wata sanarwar gwamnati ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙasashen biyu za su ba da muhimmanci ga haɗin guiwar bunƙasa layukan jirgin ƙasa.

KU KUMA KARANTA:Ƙasar China ta yi alƙawarin ba da dala biliyan 50 ga nahiyar Afirka

Sanarwar ta zo ne bayan da Firimiya Li Qiang na China ya gana da Shugaban Vietnam To Lam, a Hanoi da yammacin Asabar, a yayin da Li ɗin ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a Vietnam.

Wasu majiyoyi sun shaidawa kafar labaru ta Reuters cewa, ana sa ran a yayin ziyarar, China da Vietnam su rattaba hannu kan sabbin yarjejeniyoyi da ya hada da wadda zata bunkasa aikin layukan dogo, da kasuwancin amfanin gona.

A ranar Lahadi ake sa ran Li zai gana da Priministan Vietnam Phan Minh Chinh, ya kuma halarci wani taron kasuwanci a Hanoi.

A farkon watan nan ne Vietnam tayiwa China bore kan abinda ta kira, hari kan jirgin kama kifin Vietnam a kan ruwan kudancin China da ake takaddama a kan shi, da ya yi sanadiyyar raunata masunta da dama.

Leave a Reply