CBN zai ci gaba da ba wa gwamnati ƙayyadadden kashi 5 cikin 100 na bashi

0
60
CBN zai ci gaba da ba wa gwamnati ƙayyadadden kashi 5 cikin 100 na bashi

CBN zai ci gaba da ba wa gwamnati ƙayyadadden kashi 5 cikin 100 na bashi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jaddada matakin ci gaba da bai wa Gwamnatin Tarayya ƙasar kayadaɗɗen adadin kashi 5 cikin 100 na bashi a kasafin kuɗi na shekarar 2024 zuwa 2025.

Matakin dai ya yi hannun riga da gyaran ɗokar da majalisar ɗokokin ƙasar ta amince da shi a baya-bayan nan, wanda ya nemi a ƙara adadin rancen daga kashi biyar zuwa kashi 10.

Ƙudaɗe na ”Ways and Means”, lamuni ne da CBN yake bayarwa don tallafawa gwamnati domin amfani a yayin da aka samu gibi a kasafin kuɗi na wucin gadi kana suna da iyaka da matakan da doka ta shimfida.

A rahoton da aka yi masa take da ‘Kuɗi da Bashi da Kasuwancin Waje da Ƙa’idodin kasafin kuɗi na shekarar 2024 zuwa 2025, wanda babban bankin ya fitar a ranarTalata’, ya ce ƙa’idar ta yi daidai da na tsarin aikin Medium-Term Fiscal Framework Tool (MTFF).

A ƙarkashin shirin na MTFF, babban bankin ƙasar CBN zai sa ido kan tsare-tsare da kuɗaden da ake sa ran samu da lokuta tare da aiwatar da manufofin da suka dace tare da tallafawa shirin da zai farfado da kuma tabbatar da daidaito a attalin arzikin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: CBN ya ƙara ƙudin ruwa zuwa kaso 26.75

A wani taron kwamitin majalisar dattawa a watan Fabrairun 2024, gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa babban bankin ba zai sake baiwa gwamnatin tarayya lamunin ba har sai an biya bashin da aka karba a baya.

Olayemi ya bayyana cewa hakan na ɗaya dag cikin matakan da CBN ya ɗauka na daƙile matsin tattalin arziki da ƙasar ta fada a ciki.

Sai dai sabbin bayanan da CBN ya fitar sun bayyana cewa, “Za a ci gaba da ba wa Gwamnatin Tarayya bashin kashi 5 cikin 100 don cike gibin ayyukan kasafin kuɗin da ta tara a shekarar da ta wuce.

Kana za a ba da kuɗin da wuri sannan a biya shi ta ko wane hali a ƙarshen shekarar da aka bayar da kuɗin.”

Leave a Reply