CBN ya umarci ’yan canji su sake rajista

0
117
CBN ya umarci ’yan canji su sake rajista

CBN ya umarci ’yan canji su sake rajista

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya buƙaci ɗaukacin ’yan canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare su sake rajista domin ci gaba da harkokinsu.

Babban bankin ya bayar da wannan umarni ne a wata takarda da Daraktan Sashen tsare-tsaren harkokin kuɗi na bankin, Haruna Mustafa ya fitar a ranar Laraba.

“Ana umartar ’yan canjin su cika sharuddan babban bankin na mallakar lasisin u cikin watanni shida.

“Sannan, duk ’yan canjin su sani cewa suna da damar neman kowane irin lasisi kamar yadda doka ta tanadar,” in ji sanarwar.

Bankin ya kuma yi wasu sauye-sauye a tsarin gudanar da hada-hadar canji.

Daya daga ciki shi ne soke biyan kudin kafin alkalami na tilas har na Naira miliyan 200 ga masu lasisin mai daraja ta ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Soke lasisin dubban kamfanonin canji ba zai kawo maslaha ba – ‘Yan Canji

Haka kuma, bankin kolin ya kuma soke biyan kudin kafin alkalami na dole na Naira miliyan 50 ga masu riƙe da lasisin mai daraja ta biyu.

Bankin na CBN ya kuma soke kuɗin sabunta lasisi na shekara-shekara.

Leave a Reply