Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan wani faɗa da aka yi bayan wasan da aka yi tsakanin DRC da Maroko inda ƴan wasa da jami’an ƙwallon ƙafa suka shiga rikicin.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala wasan inda keftin ɗin DRC Chancel Mbemba da kocin Maroko Walid Regragui suka fara faɗa. Rikicin ya haifar da cece-kuce tsakanin ‘yan wasa da jami’an ƙungiyoyin biyu da suka ci gaba da barin filin.
KU KUMA KARANTA: Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Ahmed Musa, ya cika alƙawari, ya sayawa Karkuzu gida
Bayan nan, CAF ta fitar da sanarwa kan lamarin inda take cewa: “CAF ta ƙaddamar da bincike kan Royal Moroccan Football Federation da kuma Congolese Association Football Federation bayan wani lamari da ya faru bayan wasa a Gasar AFCON ta CAF da TotalEnergies a Cote d’Ivoire tsakanin Maroko da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo. “CAF ba za ta yi wani ƙarin bayani kan wannan lamarin ba har sai an kammala bincike.”