Daga shafin Muhammad Cisse na facebook
Hoton a lokacin yana tare da marigayiyar matarsa Safinatu da ‘ya’yansu; Fatima, Hadiza da Zulaihat a gidan gwamnati, a fadar mulki ta Dodan Barrack legas.
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi aure kafin matarsa ta yanzu Aisha Buhari.
Buhari tun yana matashin soja ya auri Safinatu a watan Disamba 1971, jim kaɗan bayan kammala karatunta na jami’a, kuma sun haifi ‘ya’ya biyar tare, Fatima, Hadiza, Zulaihat, Safinatu da kuma marigayi Musa.
An ce Buhari ya san Safinatu tun tana da shekara 14 kafin aurensu.
Matar Buhari ta farko Safinatu ta kasance uwargidan shugaban ƙasar Najeriya a lokacin da yake shugaban ƙasa.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Buhari ce ta jefa ‘yan Najeriya halin ƙuncin da suke ciki – Akpabio
An haifi Safinatu Buhari a garin Jos na Jihar Filato a ranar 11 ga Disamba, 1952, ‘ya ce ga Alhaji Yusufu Mani da Hajiya Hadizatu Mani wacce ta fito daga ƙaramar hukumar Mani a jihar Katsina kuma ‘yar kabilar Fulani ce ta Arewacin Najeriya.
Lokacin da Musa ‘Yar’Adua, kwamishinan al’amuran Legas a lokacin, ya naɗa mahaifinta a matsayin sakatare na musamman iyayenta sun koma jihar Legas.
Safinatu Buhari ta yi makarantar firamare da ke Tudun Wada, Jos.
A shekarar 1971 ta yi karatu a Kwalejin horas da malamai ta mata ta Katsina inda ta samu shaidar kammala karatun digiri na biyu.
Ta yi karatun Islamiyya kuma tana iya rubutu da Ingilishi da Larabci. Lokacin da Safinatu Buhari tana raye, ta kasance malamar makaranta.
Safinatu Buhari ta haɗu da Muhammadu Buhari tana da shekaru 14, kuma sun yi aure tana da shekaru 18 a duniya a shekarar 1971.
‘Ya’yansu biyar ne Tare da Muhammad Buhari
Zulaihat Buhari, Fatima Buhari, Hadiza Buhari, Safinatu Lami Buhari, da marigayi Musa Buhari.
Safinatu Buhari ta koma Kaduna da ‘ya’yanta bayan da Ibrahim Babangida ya hambarar da gwamnatin Muhammadu Buhari.
A shekarar 1988, sun rabu da mijinta na ta
*Mutuwa*
Safinatu Buhari ta rasu ne a ranar 14 ga watan Junairu, 2006, tana da shekaru 53 a duniya, sakamakon kamuwa da ciwon suga.