Buhari da Atiku sun aike da sakon Allah Ya kara lafiya ga Sheikh Ɗahiru Bauchi

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ya yiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi fatan samun sauki daga rashin lafiya.

Shugaban, a sakon da ya aikewa jagoran Ɗarikar Tijjaniyya, wanda Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ibrahim Ali Pantami ya mika a madadinsa, ya ce yana yi wa Sheikh fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya yi addu’ar Allah ya kara wa jagoran addinin Musulunci lafiya domin ya ci gaba da jagorantar mabiyansa da al’ummar kasar nan, a ƙoƙarin gina al’umma mai cike adalci da tausayi.

“Addu’ata ta gare shi, Allah ya jara masa lafiya da samun lafiya cikin gaggawa,” inji shi.

KU KUMA KARANTA:Rashin tsaro: Rarara ya shirya addu’a ta musamman a Kano

Shaikh Ali Isa Pantami ya kai rahoto ga shugaban ƙasa cewa, halin da Sheikh din ke ciki yanzu da sauki, ya ƙara da cewa jagoran na addinin musuluncin ya godewa shugaban ƙasa bisa kulawar da ya nuna masa, tare da addu’ar Allah ya ci gaba da basu nasarar gudanar da mulki, a bangaren gina kasa, zaman lafiya, da ci gaba.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar shima ya aiki da nasa saƙon nemawa shaikhin malamin sauƙi a shafinsa na tweeter.

Atiku Abubakar ya ce “Yanzun nan na sami labarin mai tada hankali cewa Sheikh Ɗahiru Bauchi shugaban Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya ba shi da lafiya.

“Bisa la’akari da irin kyakykyawan jagoranci da abokantaka da Shehin Malamin yake yi da jama’a a faɗin kasar nan, ina mika sakon fatan alheri da samun lafiya cikin gaggawa.

“Allah ya baka lafiya da gaggawa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi da fatan Allah ya kare ka, ya kuma kara maka karfin gwiwa akan cigaba da yiwa al’ummar mu hidima” in ji Atiku Abubakar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *