‘Yan ta’addar boko haram sun kai farmaki ƙauyen Jibwiwi da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno, inda suka ƙona gidaje takwas da tarin runbunan kayan amfanin gona.
Rahotanni sun ce maharan waɗanda suka zo akan babura, sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar litinin.
Wani ɗan banga a garin ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan ta’addan sun ƙona ma’ajiyar abinci da ke ɗauke da ɗaruruwan buhunan hatsi ba tare da sun dauki komai ba.
“Sun ƙona gidaje takwas da ma’ajiyar abinci mai yawa; yawancin runbunan sun ƙunshi buhunan masara da dama da gyaɗa da dai sauransu.
KU KUMA KARANTA:Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 49 a dajin Sambisa
“Daga nan suka zarce zuwa unguwar Ngulde da ke ƙaramar hukumar Askira Uba, amma mun samu nasarar murkushe su da taimakon mafarauta.
“Yunkurin gaggawar da ‘yan banga suka yi ya daƙile farmaki, yayin da ‘yan ta’addan suka tsere bayan sun ga fitulun motocin sintiri na mafarauta,” in ji shi.
Shugaban ƙungiyar ‘yan banga na Arewa maso gabas, Shawulu Yohanna, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ƙara da cewa rundunarsa ta maida martani cikin gaggawa tare da daƙile yunƙurin ‘yan ta’addan na kai hari kan al’umma na gaba.
[…] KU KUMA KARANTA:Boko haram sun kai hari ƙauyen Borno, sun ƙona runbunan abinci da gidaje […]
[…] KU KUMA KARANTA: Boko haram sun kai hari ƙauyen Borno, sun ƙona runbunan abinci da gidaje […]
[…] KU KUMA KARANTA: Boko haram sun kai hari ƙauyen Borno, sun ƙona runbunan abinci da gidaje […]