Bobrisky ya shaƙi iskar ‘yanci bayan watanni 6 a gidan gyaran hali

0
129
Bobrisky ya shaƙi iskar 'yanci bayan watanni 6 a gidan gyaran hali

Bobrisky ya shaƙi iskar ‘yanci bayan watanni 6 a gidan gyaran hali

Daga Ali Sanni

Matashin nan mai shigar jinsi biyu, wato Bobrisky, wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon wata shida sakamakon cin zarafin kuɗin ƙasa, ya shaƙi iskar ‘yanci bayan watanni shida a gidan gyaran hali na Kirikiri dake birnin ikko.

Ya shaki iskar ƴancin ne da musalin karfe goma na safiyar Litinin.

Bayan kama shi an ga Bobrisky sanye da kayan maza, amma da alama bayan an sako shi shi ya koma gidan sa na tsamiya inda aka ganshi sanye da kayan mata.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure Bobrisky bayan ya amsa laifin wulaƙanta takardar naira

A watan Afrilu ne mai shari’a Abimbola Awogboro na baban kutun tarayya dake jihar Legas ta yanke masa hukuncin wanda ya fara 24 ga watan Maris ɗin shekarar nan.