‘Bazoum bai yi yunƙurin tserewa daga Nijar ba’

0
225

Lauyoyin hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum sun musanta zargin da sojojin ƙasar suka yi cewa ya yi yunƙurin tserewa daga ƙasar.

Bazoum da iyalansa suna tsare a gidansa da ke fadar shugaban ƙasa a hannun sojojin da suka kifar da gwamnatinsa tun ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Ranar Alhamis sojojin sun ce tsohon shugaban Nijar da iyalinsa da masu dafa masa abinci da kuma wasu masu tsaron lafiyarsa sun yi “yunƙurin tserewa daga Nijar”.

An shirya ɗaukarsu daga Yamai a jirgi mai sauƙar unguwa “mallakin wata ƙasar waje” domin kai su Nijeriya, a cewar kakakin gwamnatin sojin Amadou Abdramane a saƙon da ya karanta a gidan talbijin na ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Mohamed Bazoum ya yi yunƙurin tserewa — Sojojin Nijar

Ya ƙara da cewa an daƙile yunƙurin da suka yi na tserewa kuma an “kama manyan mutanen da suke da hannu a yunƙurin da kuma masu taimaka musu”.

Sai dai wani rukunin lauyoyin Bazoum ya yi watsi da babbar murya da wannan labari da “aka kitsa” kan tsohon shugaban ƙasar.

Ana tsare da Bazoum da matarsa da dansa ba tare da ba su damar ganawa da lauyoyinsu ba, kuma ba tare da sanin abin da duniya ke ciki ba, a cewar Mohamed Seydou Diagne, kakakin rukunin lauyoyin tsohon shugaban ƙasar, a wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya ƙara da cewa sojojin da ke mulkin Nijar sun likitocin Bazoum ganawa da shi a yayin da ya kai musu abinci.

Diagne ya ce abokan hulɗar Bazoum ba su ji ɗuriyarsa ba tun ranar Laraba da daddare zuwa Alhamis.

Ranar Juma’a shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana “matuƙar damuwa game da halin rashin tabbas” da Bazoum da iyalansa suke ciki.

A watan jiya, lauyoyin Bazoum sun gurfanar da gwamnatin sojin Nijar a gaban kotun ECOWAS kan yadda ake ci gaba da tsare shi ba tare tun da aka hamɓarar da gwamnatinsa.

Leave a Reply