Bayan shekaru 5 a gidan yari, tsohon ɗan majalisa, Faruƙ Lawan, ya shaƙi iskar ‘yanci

0
66
Bayan shekaru 5 a gidan yari, tsohon ɗan majalisa, Faruƙ Lawan, ya shaƙi iskar 'yanci

Bayan shekaru 5 a gidan yari, tsohon ɗan majalisa, Faruƙ Lawan, ya shaƙi iskar ‘yanci

A ranar Talata aka sallami Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda aka tsare shi bayan samun shi da laifin karbar cin hancin Dala 500,000 da kotu ta yi a shekarar 2021.

Tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Kano, Faruk Lawan, ya fito daga gidan yarin ne bayan kammala zamam wankafin shekara biyar kan laifin karɓar cin hanci.

Kotu ta kama shi ne da laifin neman cin hancin Dala miliyan uku daga fitaccen attajiri kuma shugaban kamfanin Zenon Oil, Femi Otedola, a shekarar 2012.

Faruk Lawan ya tsinci kansa a gidan tarin Kuje ne bayan da kotu ta same shi da laifin nema da kuma karɓar cin hancin Dala 500,000.

KU KUMA KARANTA: An saki tsohon Ministan Sharian Equitorial Guinea, Ruben Maye, daga kurkuku

Ɗan majalisar ya aikata laifin ne a lokacin da tsohon dan majalisar ke jagorantar kwamitin binciken bakalar tallafin man fetur.

A watan Janairun 2024 ne Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa na zaman shekara biyar a gidan yari kan laifin karbar na-goron.

Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya ce, “Yau an buɗe wani sabon babi a rayuwata, da fitowata daga Gidan Yarin Kuje, kuma ina godiya ga Allah da Ya ba ni wanna dama.

“Na gode wa Allah da Ya bar ni a raye cikin koshin lafiya domin sake haɗuwa da iyalaina da abokan arziki. Ina matukar godiya game da hakan.

Leave a Reply