Bashin da Najeriya ta ciwo ya ƙaru zuwa tiriliyan N89.3

0
220

Daga Haruna Idi Hassan

Bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da naira tiriliyan 20.6 a sakamakon faɗuwar darajar naira a watanni biyar da Shugaba Tinubu ya yi a bisa mulki.

Aminiya ta gano, a wata guda basukan da ake bin ƙasar suka ƙaru zuwa naira tiriliyan 89.2, duba da shirin gwamnatin na ƙara ciwo bashi daga ƙasashen waje.

Hakan na nufin bashin N418,779 ke kan kowane ɗan ƙasar mai yawan al’umma miliyan 13. A watan Oktoba ne Ministan Kudi, Wale Edu, ya sanar da shirin Gwamnatin Tarayya na ciwo bashin dala biliyan 1.5 daga bankin duniya.

Idan bankin ya ba da bashin, abin da ake bin Najeriya zai karu zuwa dala biliyan 114.9, wato naira tiriliyan N89.2, abisa farashin canjin Dala na N776.4. Wannan kuma bai haɗa da shirin gwamnatin na karɓo wani bashin na dala biliyan 7.8 da kuma miliyan €100m da Shugaba Tinubu ya samu sahalewar Majlisar Dattawa a matsayin wani ɓangare na kasafin 2022-2024.

Aminiya ta gano cewa ba don ƙara faɗuwar darajar naira daga N461 da CBN ke canjin dala a ranar 30 ga watan Mayu ba, da jimillar bashin da ake bin ƙasar bai fi tiriliyan N57.6 ba.

Faduwar darajar naira da 315 a wajen canjin Dala a cikin kwanaki 30 ɗin ta sa bashin da ake bin Najeriya ƙaruwa da tiriliyan N20.6 zuwa tiriliyan 89.2.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi suna yajin aiki

Zuwa watan Yuni, bashin da ƙasar ta ciwo daga waje Dala biliyan 43.1 ne; na cikin gida dala biliyan 70.3.

Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suna bin ta Dala biliyan 20.7; ƙasashen waje na bin ta dala biliya 5.5; sai Eurobon dala biliyan 15.6; takardun amumin Dala miliyan 931 da wasu basukan na dala miliyan 300.

Daga cikin basukan ƙasashen waje na dala biliyan 43.1, ana bin gwamnatin tarayya biliyan 38.8, jihohi da Birnin Tarayya Dala biliyan 4.3.

Jihohi mafiya cin bashi

Jihohin da aka fi bi bashi a cikin dala biliyan 4.3 su ne:

  1. Legas — Dala bilyan 1.2
  2. Kaduna — Dala miliyan 569
  3. Edo — Dala miliyan 258
  4. Bauchi — Dala miliyan 170
  5. Kuros Riba — Dala miliyan 153

Mafiya ƙarancin bashi:
Waɗanda bashinsu ya fi ƙaranci su ne:

  1. Borno — Dala miliyan 18m
  2. Taraba — Dala miliyan 21
  3. Yobe — Dala miliyan 21
  4. Jigawa — Dala miliyan 26
  5. Binuwai — Dala miliyan 29
  6. Filato — Dala miliyan 31.

Leave a Reply