Bankuna za su fara raba katin ATM mai haɗe da katin ɗan ƙasa – Gwamnati Najeriya

1
450

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a yanzu ‘yan Najeriya suna da damar neman bankunansu su riƙa ba su katin cirar kuɗi na ATM wanda yake haɗe da bayanan katin ɗan-ƙasa, wato na komai-da-ruwanka kenan.

Ministan sadarwa Farfesa Isa Pantami, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce babu wani kuɗi na daban da mutum zai biya a kan hakan.

KU KUMA KARANTA: Masana kimiyyar sadarwa sun yaba wa NCC kan samar da lambobin bai ɗaya

Pantami ya ce an samu amincewar yin hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ministan ya ce an bayar da damar hakan ne sakamakon takardar da hukumar da ke yin katin ɗan-ƙasar ta gabatar na neman a amince bankuna su rinƙa yin katin banki wanda kuma za a iya amfani da shi na a matsayin na ƙan-ƙasa.

1 COMMENT

Leave a Reply