Bani da niyyar fice wa daga jam’iyyar APC – Inuwa Waya

0
5
Bani da niyyar fice wa daga jam'iyyar APC - Inuwa Waya

Bani da niyyar fice wa daga jam’iyyar APC – Inuwa Waya

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Malam Inuwa Waya, dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023, a karkashin jam’iyyar APC, ya tabbatar da cewa ba shi da niyyar ficewa daga jam’iyyar.

Waya, wanda ɗan siyasa ne kuma mai taimakon al’umma , ya baiyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya ke tattaunawa da wani dan jarida a Kano, inda ya ce ya amince da aƙidun jam’iyyar APC, don haka bai ga dalilin ficewa daga jam’iyyar ba.

A cewar Waya, duk da cewa bai fitar da rai ba, amma sauya sheƙa wata jam’iyyar siyasa abu ne da mai kamar wuya, duba da irin kyakykyawan tsarin da jam’iyyar APC mai mulki a kasar ke da shi.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin APC ce ke ɗaukar nauyin rikicin da ke faruwa a jam’iyyun LP, PDP da NNPP – El-Rufai

“Na yi imani da ka’idoji da akidu na APC. In dai babwani juyi aka samu ba, ban ga dalilin sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba.”

“Ba na fitar da rai,, amma ina cewa sai dai idan akwai wani abu da ya faru, amma a yanzu, ba na tunanin barin APC Kuma na gamsu da ita.

“Ni masoyin jam’iyyar APC ne kuma a shirye nake in ba da gudunmawata ta kowace hanya,” in ji shi.

Da ya ke ƙarin haske kan fita daga takarar zaɓen 2023, Waya ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kan jam’iyya, inda ya kara da cewa ya bayar da gudunmawa sosai ga jam’iyyar a lokacin yakin neman zaɓen.

Leave a Reply