Bana cajin ƙasa da naira miliyan ɗaya a kowane fim- Hadiza Gabon

0
583

Fitacciyar jarumar Kannywood, haifaffiyar kasar Gabon, Hadiza Aliyu Gabon, ta bayyana dalilin da ya sa ba a fiye ganin ta a fina-finan Hausa ba, ta ce hakan na faruwa ne saboda ta zama fitacciyar jaruma kuma a yanzu ba ta karɓar ƙasa da Naira miliyan 1 ga kowane fim da ake so ta fito.

“Na yi nisa a harkar, kuma na ba da duk abin da zan iya don ci gaban masana’antar, kuma nayi aikin wasan kwaikwayo sama da shekaru 10, mutum ya kai matakin da, sai kayi shawara kan farashi mai ma’ana kafin ka amince da kuma sa hannun a duk wata kwangilar aiki, Hadiza Gabon a yanzu tana cajin daga miliyan 1 zuwa sama, idan ba za ku iya biya ba, to ba wani aiki dan za muyi tare”in ji ta.

Da take magana da wasu wakilan kafafen yaɗa labarai a Kano, a sabon ofishinta na tashar Youtube, mai suna ɗakin Gabon, ta ƙara da cewa ta yanke shawarar buɗe tashar Youtube domin gabatar da wasu mutane, ta yi diploma a Faransanci daga Jamhuriyar Gabon , amma ta yi alkawarin shiga Jami’ar Bayero, Kano nan ba da dadewa ba, don wani shiri na wucin gadi a fannin sadarwa ko aikin jarida.

KU KUMA KARANTA:Jarumar Kannywood Dawayya ta buɗe katafaren kantin sayar da kayayyaki a Kano

“Idan Allah Ya sa nayi aure , zan sake mayar da hankali kan sana’ata, tare da yarjejeniya da mutumin da zan aura, amma ko shakka babu zan ci gaba da sana’ar nishadi ko tallace-tallace, ni na zo Najeriya kusan ba tare da wani abin faɗa ba amma kamar yadda kuke gani, Gabon a yanzu ta zama jarumar wasan kwaikwayo, ina matukar godiya ga masoyana da kuma ‘yan Najeriya gaba daya, nan ba da jimawa ba, zan shiga harkar talabijin na zama wata Winfrey Operah.

“Masana’antar Kannywood na ci gaba da haɓaka cikin sauri, amma zan iya gaya muku, wannan sabuwar sigar shirya fina-finai ba ita ce hanyar da ta fi dacewa ta bunƙasa masana’antar ba, har yanzu muna bukatar shirya fina-finai na mako-mako maimakon jira na tsawon makwanni ko wata don shirin fim wanda ya dace,mai yiwuwa ma ba zai jawo hankalin masu kallo ba, don haka zan duba batun shiga cikin shirin fim na al’ada” in ji ta.

Leave a Reply