Wata mata ‘yar jihar Delta mai shekaru 33 mai suna Ifeoma Ossai, wacce rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama, bisa zarginta da laifin damƙar azzakarin mai gidan ta ke haya, a lokacin da ta yi artabu da shi har ya mutu, ta shaida cewa ko kaɗan bata taɓa azzakarin marigayin ba
Da ta ke bayanin yadda ta karɓi gidan hayar ta ce ta biya naira dubu 210 ne kudin keɓanɓɓan ɗaki guda a gidan inda aka ce a duk shekara zata dinga biyan naira dubu 110, Naira dubu 100 kuma da ya bayar ladan jami’in da ya kawo ta gidan ne.
“Lokacin da na isa gidan, na gano cewa babu ruwan famfo ko na rijiyar burtsatse, na gaya musu ba zan iya biyan kuɗin gidan ba saboda ba zan iya wahalar neman debo ruwa a kan tituna ba, sai mai gidan ya yi alkawarin yin rijiyar burtsatse a gidana. Don haka, na gamsu kuma na biya, kuma daga baya mai gidan ya ƙi bai wa wakilansa wanda ya kawo ni kasonsa na kuɗin, kuma hakan ya tilasta na sake biyan ƙarin naira dubu 20, Ban kuma tare a gidan a kan lokaci ba, saboda ba zan iya zama ba tare da samar da ruwa ba.
KU KUMA KARANTA: Yadda mace ta yanke azzakarin mijinta, ta kashe shi har lahira
Na gaya masa cewa ina da matsalar ƙirji, dalilin da ya sa ba zan iya fita ina ɗebo ruwa a waje ba, inda ya roke ni da in ba shi makonni biyu don ya warware matsalar ruwa a gidan ya kuma kira ni daga baya domin na shiga gidan ko da nazo sai na tarar babu rijiyar burtsatsen, ko da na tambaye shi, sai ya ce mini suna jiran wanda zai yi hayar sauran ɗaku nan gidan, amma duk wanda ya zo gidan sai ya koma ya ƙi karɓa saboda babu ruwa a gidan, na kuma kawo mutane hudu don su duba gidan don kawai su taimaka wajen aikin, amma ba su yarda su zauna ba saboda babu ruwa, a wata na shida na sake fuskantar shi, a lokacin ne ya ce min mahaifiyarsa ce za ta zo ta zauna gidan, a wata na takwas, na kira mahaifiyar wacce ita ce ta ke da gidan, na yi korafin cewa na gaji da zama babu ruwa a gidan domin debo ruwan da nake yana shafar lafiyata saboda ina da ciwon ƙirji , sai matar ta ce min ta ba ɗanta (marigayin) kuɗi domin a yi rijiyar burtsatse, ta kuma ce in samo ma’aikacin famfo don fara aikin tona rijiyar,na ce mata ba aikina ba ne; tana da yara maza huɗu,su ya kamata ta baiwa aikin nemo masu aikin famfon, sai daga ta yi tayi alƙawarin yin hakan kuma bayan kwana uku suka fara aikin tona rijiyar, hakan ne yasa na yi murna kwarai har na sayi abun sha na raba a gidan saboda murnar ganin an fara aikin rijiyar burtsatsen” in ji ta.
Ta ce murnar ta koma ciki a lokacin da ta fahimci basu janyo ruwan zuwa ɓangaren gidan da take haya ba, “nan sake yin ƙorafi aka ce min ba za a iya yin komai a kai ba, wai ƙorafina yayi yawa, na tuna masa (mai gida) yarjejeniyar da muka yi lokacin da na yi hayar gidan, amma yayi burus, sai na yanke shawarar zan zauna gidan na ɗan lokaci kafin kudin hayata ya ƙare na ƙaura daga gidan, na nemi wani, inda nayi baƙin cikin kama gidan.”
Idan baku manta ba, jaridar Neptune Prime Hausa ta kawo maku labarin zargin da ‘yan sanda suka yi wa matar cewa tayi ta jan azzakarin mai gidan da take haya a lokacin da suka kaure da faɗa lamarin da yayi sanadiyar mutuwarsa, sai dai matar ta musanya hakan, ta ce ko kaɗan bata taɓa azzakarinsa ba, ta ce a ranar Asabar da lamarin ya faru, tana dawowa daga wani wuri sai suka ce ta biya naira dubu ɗaya kuɗin wutar lantarki saboda ana amfani da na’urar jan ruwan rijiyar burtsatse a gidan.
“Mun yi amfani da wutar lantarki na tsawon kwanaki huɗu zuwa biyar saboda akwai masu haya 12 a gidan, don haka sai na je wajen mai gidan na tambaya dalilin da ya sa muka ci wutar lantarkin naira 12,000 a cikin kwanaki biyar kacal.
“Na kuma tuntubi wani abokina da ke aiki da kamfanin wutar lantarki, ya ce ko dai an tara bashi a kan mitar ko kuma mutumin bai biya N12,000 ba, amma na ce masa na amince da mai gidan, kuma ba zai iya biyan ƙasa da adadin ba, don haka, na je wurinsa na tambaye shi ko akwai bashi a lissafin, sai ya amsa, nan take na biya Naira 1,000 na fita, amma da na isa gida babu ruwa babu hasken wutar lantarki, duk mutanen gidan sun ɗebi ruwan kafin zuwana, don haka sai na kai ƙara wajen kaninsa cewa yaudara ce kuma rashin adalci ne, sai ya roƙe ni ya ce nayi haƙuri, ya ce ba zai iya yi wa ɗan uwansa magana a kai ba, domin bai taɓa sanin komai game da gidan ba kuma basa magana da yayan nasa, kuma na san cewa dukansu ba sa magana; hatta matansu ba sa magana da juna”. Inji ta.
Ta ce mai gidan, ranar litinin ya fito ya kawo min hari yana ƙokarin far mata da duka, saboda ya ji tana cewa ta daina biyan ko wane kuɗi har sai kuɗin hayarta ya ƙare ta fita daga gidan, biya ba idan kudina ya kare.
“Ya ce idan ba zan biya ba, in shirya kaya na na fita, matar shi ta shiga ta fara ƙirana karuwa, nan da nan lamarin rikiɗe zuwa faɗa, sai mutumin ya mare ni,matar tayi ta duniyar fuskata da jikina, ƙanensa, Daddy David, ya shiga tsakani, kuma ya gargadi ɗan uwansa da ya daina faɗa saboda yanayin lafiyarsa, domin shi (Daddy David) ya ce ɗan uwansa yana da hawan jini kuma faɗa zai iya tayar masa da ciwon, don haka sai ya tafi amma matar ta ci gaba da zagina duk da irin raunukan da suka yi min, don haka, na je wurinta na yi mata duka, daddy David ya bar ni na yi mata duka har na gamsu kafin ya raba mu, amma muna cikin haka sai na ji mijinta ya yi waya yana cewa wasu su fara zuwa gidan bayan rashin jituwar na koma falo na na yi shirin zuwa wurin ’yan sanda don ba da rahoton lamarin da jini a fuskata, amma bayan minti 30, na ji mutane suna kururuwa, don haka na fita sai daddy David yace mai gidan ya faɗi, na garzaya cikin gidansu sai naga mutumin (mai gidan) a sume, yana cikin halin yin ƙira saboda wayar na hannunsa ya kai ta kusa da kuncinsa kamar yana kira, daga nan suka garzaya da shi asibiti, kuma a can ne ya mutu, suka dawo da shi gida kowa yana cewa mutumin ya san yana da hawan jini kuma har yanzu ya ci gaba da faɗa”. In ji ta.
Ta kara da cewa ta san cewa shi kaɗai ne a cikin ɗaki lokacin da ya ya shiga wannan halin, “don haka, na zauna a gidan har suka kawo ‘yan sanda domin na san ban kashe shi ba sai suka shaida wa ’yan sanda cewa ya fadi ne bayan faɗa, sai na yi mamaki washegari da suka fara cewa na damƙe masa azzakarinsa, nayi mamaki sai na tambayi ɗan uwansa me yasa yayi ƙarya saboda yaga duk abinda yafaru tsakaninmu, har ila yau ba abin da ya faɗa a gidan radiyo ke nan ba yau kwana ɗaya, to, me yasa canza magana?
Matar ta ce ta yi nadamar duk abin da ya faru kuma da ta sani, da ta bar shi lokacin da ya fuskance ta, “da na kai rahoto ga ’yan sanda lokacin da ya mare ni, amma Allah yana fahimtar komai,ko da aka garzaya da shi asibiti, na shirya zan kai rahoto a ofishin ‘yan sanda domin idan ya dawo ‘yan sanda su sasanta mu, amma kash sai aka ce ya mutu”. in ji ta.