Bai kamata ku kai ‘ya’yanku makarantar kwana ba saboda ku sami sukuni – Malamar Coci

0
235

Matar babban limamin cocin Living Faith ta Winners, Faith Oyedepo, a cikin sakon da ta wallafa kwanan nan a Facebook inda ta tura sako ga jama’a, ta bayyana wasu dalilai da tace bai kamata iyaye sukai ‘ya’yansu makarantar kwana ba.

A cewar ta, wasu iyaye a ƙoƙarinsu na samun karin lokaci na harkokin kasuwanci da sauran abubuwan da suka shafi kansu, suna tura ‘ya’yansu makarantun kwana.

Wannan ba wai an ce makarantun kwana dukan su ba su da kyau ba, amma idan dalilin tura ‘ya’yanku shi ne don ku sami lokacin kanku, to ba daidai ba ne, ko da ko wani irin makarantar kwana da zaku kai su.

KU KUMA KARANTA:Bikin Sallah: Wata Cocin Kaduna Ta Raba kayan sawa, Kayan abinci Da Tsabar Kudi Ga Marayu Sama Da 50

Wannan yana nufin cewa iyaye su horar da ‘ya’yansu ba kawai ta hanyar samun nasarar ilimi ba, “amma kuma a tafarkin Ubangiji mahallici, kuma yayin da kuke yin haka a cikin wannan sabuwar shekara mai zuwa Allah zai ba danginku mamaki” inji ta.

“‘Ya’yanku za su zama abin nuni ga sauran yara, ina kuma shelanta kan rayuwarsu cewa Allah zai ɗaukaka su sama da takwarorinsu.

Kuma yayin da suke girma cikin hikima, Allah ya ci gaba da taimaka masu.

Leave a Reply