Badaru Abubakar ya yi murabus daga ministan tsaron Najeriya 

0
76
Badaru Abubakar ya yi murabus daga ministan tsaron Najeriya 
Alhaji Badaru Abubakar

Badaru Abubakar ya yi murabus daga ministan tsaron Najeriya

Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take, yana mai bayyana dalilan lafiya a matsayin abin da ya tilasta masa yin hakan.

A cikin wasikar da ta dauki ranar 1 ga Disamba, wadda aka aika wa Shugaba Bola Tinubu, tsohon ministan ya ce dole ne ya bar kujerar don kula da lafiyarsa. Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin nasa tare da yaba masa kan hidimar da ya yi wa ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya naɗa Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro

Ana sa ran Shugaban Ƙasa zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru cikin mako mai zuwa.

Badaru Abubakar, mai shekaru 63, ya yi gwamna a Jihar Jigawa na tsawon lokaci biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin a naɗa shi Ministan Tsaro a ranar 21 ga Agusta, 2023.

Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin ƙasa, inda ake jiran ƙarin bayani kan matakan da gwamnati za ta dauka nan gaba.

Wannan sanarwa ta fito ne daga Bayo Onanuga, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan yaɗa labarai.

Leave a Reply