Babu wasu da su ke juya gwamnati na – Tinubu

0
68
Babu wasu da su ke juya gwamnati na - Tinubu

 

Babu wasu da su ke juya gwamnati na – Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa babu wasu rukunin mutane ko wata ƙungiya da ke juya gwamnatin sa har su yi tasiri a sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasar.

Shugaban ya kuma jaddada cewa shi ne ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensa da kansa ba tare da wani hakki na mutane ko hukumomi ba.

A yayin ganawarsa da tawagar shugabannin addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Bala Lau a fadar gwamnati a ranar Alhamis, Tinubu ya danganta nasarar zaɓen da ya samu da sa hannun Ubangiji, da tsare-tsare da kuma goyon bayan ƴan Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya roƙi ‘yan Najeriya da su dakatar da shirin zanga-zanga

“Babu wasu mutane da ke juya gwamnatina da ake kira da ‘cabal’. Ba ni da waɗanda suka tallafa min ko kuma ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓe na, duk wani kuɗi da aka kashe lokacin yaƙin zaɓena daga aljihuna suka fito, a wasu lokutan ma, irin ƙalubalen da na fuskanta a lokacin sai a hankali, amma Allah Madaukakin Sarki ya riga ya ce ni zan zama shugaban Najeriya.” in ji Tinubu.

Shugaban ya kuma jaddada buƙatar mayar da hankali kan makomar ‘yan ƙasar, inda ya ce, “Abin da ya kamata ya mu sanya a zukatanmu shi ne makomar ‘ya’yanmu.
Muna da abubuwa da yawa da za mu koya musu a kan abin da ake bukata don zama ɗan ƙasa nagari.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here