Babbar kotu a Legas ta soke sayar da jirgin saman Najeriya Air ga Ethiopian Airlines

0
84
Babbar kotu a Legas ta soke sayar da jirgin saman Najeriya Air ga Ethiopian Airlines

Babbar kotu a Legas ta soke sayar da jirgin saman Najeriya Air ga Ethiopian Airlines

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a jihar Legas ta dakatar da cinikin sayar da jiragen sama na Nigeria Air wa kamfanin jiragen Ethiopian Airlines a ranar Litinin.

Hukuncin kotun ya biyo bayan ƙarar da Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama ta Najeriya (AON) da wasu masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama su biyar suka shigar a kan Nigeria Air.

Mai Shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ya bayar da umarnin a dakatar da shirin gwamnatin tarayya na samar da kamfanin sufurin jiragen sama na Nigeria Air.

Kazalika hukuncin kotun ya amince da duk wasu sausauci da masu ƙarar suka nema, amma ban da neman a biya su diyyar Naira biliyan biyu.

Daga cikin waɗanda suka shigar da ƙarar har da amintattun masu gudanar da harkokin jiragen sama a Najeriya da suke da rajista da kuma kamfanin Azman da Air Peace da Max Air da United Nigeria Airlines da kuma Topbrass Aviation Limited.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu ɗaga tutar ƙasar Rasha

Waɗanda ake tuhuma kuma sun haɗa da Nigeria Air Limited da Ethiopian Airlines da tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Sanata Hadi Sirika, da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya, da kuma tsohon babban ministan shari’a a Nijeriya, Abubakar Malami.

Masu shigar da ƙara sun nemi a ba su umarnin soke duk wani tsari na neman cancanta na samun aikin jiragen Nigeria Air, da kuma amincewa da kuma zaɓin kamfanin Ethiopian Airlines da ake zargi.

Leave a Reply