Babban limamin masallacin Jos ya rasu

0
135

 

Babban limamin masallacin Jos ya rasu

Wata sanarwa daga sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar JNI a jihar Filato, Sani Mudi, yace Sheihk Muhammad Lawal Adam ya rasu yana da shekaru tamanin (80) a duniya.

Allah ya yi wa babban limamin masallacin Jos ta tsakiya Sheikh Muhammad Lawal Adam rasuwa a yammacin yau, Alhamis, 11 ga Yulin 2024, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Wata sanarwa daga sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar JNI a jihar Filato, Sani Mudi, ya ce Sheihk Muhammad Lawal Adam ya rasu yana da shekaru tamanin a duniya.

KUMA KARANTA:Wata makaranta a Jos ta rushe da ɗalibai suna zana jarabawa

Sanarwar ta ce malami ne ƙwararre, masanin shari’a na Musulunci, sanannen mai tafsiri na Alkur’ani mai girma kuma jagoran al’ummar Musulmi.

An naɗa shi mataimakin babban Limamin a shekara ta 2009 sannan kuma aka naɗa shi Babban Limamin a shekarar 2015.

Za a yi jana’izarsa yau Juma’a 12 ga Yulin da muke ciki da safe bayan sallar jana’iza.

Al”ummar Musulmin Jos sun yi matuƙar kewar wannan malami da ake girmamawa.

 

Leave a Reply