Babban Hafsan Soji, Taoreed Lagbaja ya rasu

0
78
Babban Hafsan Soji, Taoreed Lagbaja ya rasu

Babban Hafsan Soji, Taoreed Lagbaja ya rasu

Shugaban sojin ƙasa, Laftar Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu yana da shekara 56 a duniya.

Wata sanarwar da mai taimaka wa shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan watsa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Janar Lagbaja ya rasu ne a Legas ranar Talata da daddare bayan jinya.

Lagbaja dai ya fara aikin soja ne a lokacin da ya fara karatu a makarantar hora da sojoji na Najeriya da ke Kaduna a shekara 1987 kuma ranar 19 ga watan Satumban shekarar 1992 ne ya zama hafsa mai muƙamin Lutanan Na Biyu.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu na taya sojin Najeriya da iyalan mamacin jimamin rashinsa.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya yi wa babban hafsan Sojin Ƙasa na riƙo ƙarin girma

Kwanan nan ne dai aka naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin muƙaddashin shugaban sojin ƙasa na Najeriya, kuma jiya ne shugaba Tinubu ya ƙara masa girma zuwa muƙamin Laftanar Janar.

Leave a Reply